. Alamu Sun Nuna Cewar Za'a Iya Sallamar Jose Mourinho - hausanet hausanet





Wednesday, 10 October 2018

Home Alamu Sun Nuna Cewar Za'a Iya Sallamar Jose Mourinho

Subscribe Our Channel





Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United wadda yanzu
yake horas da tawagar Kungiyar kwallon kafa na kasar Wales dake Birtaniya, maisuna Ryan Giggs, ya roki mahukunta a kungiyar da su kara




hakuri kada su sallami mai horar da 'yanwasan kulob din Jose Mourinho.
A cewar Giggs duk da Manchester United na fuskantar kalubale a halin yanzu, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa lamarin zai sauya,



kuma nasara zata sake zuwa kungiyar.
Kocin Mourinho, na fuskantar suka daga ciki da wajen kungiyar ta United, wadda ya hada da magoya bayanta, ganin yadda ya jagoranci wasanni hudu, ba tare da samun nasara ba a
gefe guda.




A yayin da yake fuskantar rashin jituwa
tsakaninsa da danwasan tsakiyar kulob din Paul Pogba, dan wasan da yafi kowa tsada a kungiyar. A baya bayan nan dai wasu masu fashin baki
kan harkar wasanni, sun furta ra'ayin su na





cewa, zai yi wahala a ce kungiyar ta United bata sallami Mourinho ba, mutane da dama na zaton cewa kila tsohon mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ne zai maye gurbinsa. Inda wasu jaridu suka wallafa cewa Zidane yanzu haka yana koyan iya magana da harshen
turanci domin komawarsa Manchester United a
kasar Ingila.