. Budurwar Ronaldo Ta Goyi Bayan Sa - hausanet hausanet





Wednesday, 10 October 2018

Home Budurwar Ronaldo Ta Goyi Bayan Sa

Subscribe Our Channel


Budurwar zakaran dan
wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo,
Goergiana Rodriguez, ta wallafa sakonta na goyon baya duk da zargin da ake masa na yiwa wata fyade a birnin Las Vegas, da ke Amurka.



Kathryn Mayorga, tana zargin shahararran dan wasan Juventus, da yunkurin yin lalata da ita ba tare da amincewar ta ba a cikin dakin Otel
dinsa a shekarar dubu biyu da tara.


Lauyoyin dan wasan sun musanta wadannan zarge-zarge da ake yi a kansa. Yanzu mayorga, ta shigar da kara akan tsohon dan wasan kungiyar Manchester United. A wani sakon
Instagram da Ronaldo ya tura ya nesanta kansa da zarge-zargen da ake masa inda yay a ce labaran karya ne kawai. Kuma yanzu abokiyar zamansa ta bayyana



cikakkaen goyon bayyanta, tare da tura sako ta shafinta na Instagram, na nuna soyayya. Rodriguez ta rubuta cewa “Ko yaushe kana kokarin ka canza matsalolin dake tunkararka
domin nuna cikakken kwazon da kake dashi