. Yawancin Furodusoshi Sun Sauya Akala Duba Da Sauye-Sauye A Kannywood - hausanet hausanet





Thursday, 11 October 2018

Home Yawancin Furodusoshi Sun Sauya Akala Duba Da Sauye-Sauye A Kannywood

Subscribe Our Channel




Kamal S Alkali, ya ce
tun bayan ziyartar hausanet.ml da yayi a baya sabon abin da ya faru da sana’arsa shine ya
fito da wani sabon shiri da yayiwa lakabi da daga jarumanku", sannan ya ce yanzu masu shirya fina finai sun fi mayar da hankali wajan wallafa shiryeshiryensu a tashoshin Youtube. Ya ce da dama furodusoshin fina-finai sun sauya sheka duba da yadda ake ta samun
sauye-sauye a Kannywood




, duba da ganin
cewar ta nan ma ana samun kudi, ya ce yanzu babban abinda ya dace shine, wayar da kan masu shirya fim domin tafiya dai-dai da
yadda wannan sabuwar kasuwa ta ke.



Kamal, ya ce tabarbarewar kasuwar
masana'anta a hannu guda ta dakushe
masana'antar, a wani bangaren kuma ya fadada cigaban zamani da tafiyar da yadda duniya take
a yanzu. Shafin youtube, shine shafin da akewa dafifi a yanzu amma sai dai abin dubawa shine, sai
mutum na da yawan mabiya ne sannan zai fara samun kudi, muddin jarumi bashi da mabiya toh lallai ba wani alhari da zai samu. Daga karshe ya bayyana cewa ya shiga gasar



Africa viewers award AMVCA, inda ya samu certificate na cancanta wanda a cewarsa wani
cigaba ne a bangarensa.