. Rabiu musa kwankwaso Zan doke Buhari cikin ruwan sanyi a zaben 2019 - hausanet hausanet





Friday, 12 October 2018

Home Rabiu musa kwankwaso Zan doke Buhari cikin ruwan sanyi a zaben 2019

Subscribe Our Channel




Tsohon gwamnan jihar Kano kuma
daga daga cikin yan takarar shugaban
kasa na jam'iyar PDP, Sanata Rabiu
Musa Kwankwaso, yace zai doke
shugaba Buhari cikin ruwan sanyi
idan ya zama dan takarar jam'iyar sa
a zaben 2019.




Dan majalisar dattawan yayi wannan
ikirari ne yayin da jirgin neman
zaben sa ya kai ziyarar jihar filato
ranar alhamis 27 ga watan satumba.
Jagoran tafiyar Kwankwasiya yace
yana da darajan kwato tutar mulki
Yana mai cewa "idan na zama gwanin
PDP , ni zan zama shugaban Nijeriya



Kwankwaso yayi ikirari cewa yana da
dinbim magoya a yankin arewa
yamma kuma yawan su zai karu
muddin jam'iyar PDP ta bashi damar
zama dan takarar ta.
Ya kuma soki gwamnati mai mulki ta
APC inda yace ta gaza kawar da
yunwa da rashin aikin yi da ake fama
da ita a kasar. Yayi alkawarin samad da
ingantacciyar ayyukan cigaba da
kuma tabbatar da tsaro tare da bunkasa harkar ilimi



Yace zai kwatanta kwatankwacin
tsarin ilimi na kyauta da yayi sanda
yake gwamnan Kano idan ya zama
shugaba. Kwankwaso ya kuma yi alkawarin gina hanyoyi da gadaje domin
tallafawa safarar mutane da kaya.
hannun jam'iyar APC a zaben gobe