. Bada Da Fim Kadai Na Dogara Ba Inji Aisha Tsamiya - hausanet hausanet





Friday, 12 October 2018

Home Bada Da Fim Kadai Na Dogara Ba Inji Aisha Tsamiya

Subscribe Our Channel




Jarumar Finafinan Hausa A'isha Aliyu Tsamiya, tana ɗaya daga cikin jarumai mata 'yan fim da suka halarci aikin umarah a asa mai tsarki a bana. Jarumar dai ita ce wadda ta ɗauki nauyin
ƙayataccen shirin nan mai suna "

KALANDANGI

 wanda ya fita kasuwa a shekarar da
ta gabata Jarumar, wadda yanzu ta ɗan dakata fitowa a Finafinan Hausa, hakan yasa ake ganin kamar ta rage samun kuɗi har ma wasu suna tambayar wai da wane Kuɗi ta je aikin Umarah?


Mun tattauna da jarumar a lokacin da ta ke
ƙasa mai tsarki wurin ibadah.
Bayan sun yi mata fatan alheri, sai kuma
suka tambayeta a kan wai mutane na
tambayar da wane kuɗi ta je aikin Umarah kasancewar ta rage fitowa a cikin Finafinan Hausa. Sai jarumar ta ce: 


 Dukkan yabo da godiya
su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) game da tambayar da aka yi min ni dai na kasance ba wai ga harkar fim kawai na dogara ba.Ina yin Sana'oi na saye da sayarwa kayan da na ke sayowa a ƙasar waje. Ko iya kasuwancin saye da sayarwa ɗina na riƙe ya ishi su biya mani buƙatuna na yau da kullum


Don haka ya kamata jama'a su sani ba wai ga fim kawai na dogara ba.