Dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard ya sake haifar da shakku kan yiwuwar cigaba da zamansa a kungiyar, inda dan wasan yace har yanzu, yana
son komawa Real Madrid, duk da irin bajintar da
yake nunawa a Ingila bayan soma kakar wasa ta bana.
Hazard ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin
da Chelsea ta samu a farkon kakar wasa ta bana
kan dukkanin wasannin da ta buga ba tare da yin
rashin nasara a koda wasa daya ba, wanda hakan
ya baiwa kungiyar daman darewa saman teburin
gasar Premier, tare da takwarorinta na Liverpool,
da Manchester City.
Hazard dan kasar Belgium, ya zama dan wasa na
biyu mafi kwazo a gasar cin kofin duniya da Rasha
ta karbi bakunci, bayan jagorantar kasarsa zuwa
matsayi na uku a gasar.
Cikin bayanin da Hazard yayi a baya bayan nan,
dan wasan ya ce lokaci yayi da zai fuskanci
sabon kalubale na komawa Real Madrid,
kungiyar da ya dade yana muradin kasancewa
tare da ita.
Tuesday, 9 October 2018
Subscribe Our Channel
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.