Barcelona ta kafa tarihin zama kungiya ta farko a
kakar wasannin da ta gabata, da ta bayyana
samun ribar da ta zarta dala biliyan guda.
Tun a ranar Talata da ta gabata Barcelona ta
kammala tantance ribar da ta samu a kakar wasa
ta 2017/2018 da yawanta ya kai dala biliyan da
miliyan biyar.
Karo na biyar kenan Barcelona na samun
hauhauwar riba dangane da kudaden shigar da take
samu a karshen kowace kakar wasa.
Barcelona ta ce karin ribar da ta samu na wannan
lokacin, ya dogara ne akan yarjejeniyoyin haska
wasanninta na gasar zakarun turai a kafafen
talabijin, da ta kulla da hukumar UEFA, sai kuma
cinikin sayarda dan wasanta Neymar ga Paris St
Germain akan euro miliyan 222, cikin watan
Agustan 2017.
A kakar wasa ta bana kuwa kungiyar Barcelona
ta bayyana kasafin dala biliyan 1 da miliyan 105
domin gudanar da harkokinta. Kungiyar ta kara
da cewa zuwa ranar 30 ga watan Yuni, ana binta
bashin dala miliyan 181 da dubu 300.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.