. Kuskurai: 6 Shida da akai acikin Film din FUSKA BIYU - hausanet hausanet





Saturday, 20 October 2018

Home Kuskurai: 6 Shida da akai acikin Film din FUSKA BIYU

Subscribe Our Channel




Kurakurai:
1- Lokacin da Ubale ya raka budurwar sa gida, me kallo yaga lokacin da Ubale ya bata kudi har Rashida tayi korafin cewa kudin sun kai adadin cinikin sa na ranar, sai Ubale yace dubu hudu ce ai, amma bayan Rashida ta koma gida a sanda iyayen ta suke jayayya akan kudin da Ubale ya bayar, me kallo yaji lokacin da mahaifin ta yake cewa don yaro yayi kyautar Dubu Uku meye a ciki. Tunda an nuna kudin da Rashida ta kawo a hannun
mahaifin nata, shin bai san cewa dubu hudu aka bata ba dubu uku ba?

2- Lokacin da wani matashi yazo siyan kifi yaga agogo me tsada a hannun Ubale, wanda dalilin hakan yasa yaje ya sake tahowa da
sauran abokan sa don su tabbatar da abin da suke zargi, amma bayan sun dawo sai aka ga.babu agogon a hannun Ubale. Shin Ubale yasan matashin zai sake dawowa ne da har ya cire agogon? Tunda ba’a nuna wata ‘yar tazara me nisa a tsakanin sanda matashin yaga agogon hannun Ubale da sanda yaje ya dawo ba, ya dace a samar da dalilin da yasa bayan dawowar matashin da abokin sa ba’a sake ganin agogon ba a hannun Ubale.

3- Lokacin da Bilya me wankin takalmi (Lawan.Ahmad) yaje ya bude boot din motar Alhaji Sani don dauko takalman sa da za’a wanke, bayan Bilya me ya bude boot din me kallo
yaga lokacin da ya firgita gami da dago kai yana kallon boot din cikin tsoro, kafin daga bisani da ya dau waya ya soma kira. Shin me Bilya ya gani a cikin boot din motar wanda ya
firgita shi? Tunda an nuna Bilya matsayin jami’in tsaron farin kaya, to ya dace a nunawa.me kallo abinda ya gani a motar wanda ya firgita shi.

4- Lokacin da asirin Ubale ya tonu a wajen daurin aure sanda jami’an tsaro suka biyo sa gami da harbin sa da bindiga a kafa, bayan Ubale ya shiga dakin sa ya hada kaya zai
gudu, me kallo yaga sa’in da Bilya ya shigo cikin dakin ya rutsa shi da bindiga sannan ya tafi dashi. Sam bai dace Bilya yazo ya kama
babban mai laifi irin Ubale shi kadai ba, ya dace ace Bilya sun zo kama Ubale tare da wasu abokan aikin sa, domin a yadda aka nuna Ubale mara tsoro kuma jajirtacce, to zai
iya guduwa daga hannun Bilya saboda bindigar da ya nuna masa ba lallai ne ta tsorata shi ba.

5- Kwatsam me kallo sai yaga an nuno wasu yan daba wadanda jami’an tsaro suka kama.su suna tuhumar su don su fada musu inda
wani mutum mai suna Dijango yake. Shin ta ya akayi jami’an tsaro suka fahimci cewar Ubale yana da alaka da wadannan ‘yan daba? Ya dace a nuna wa me kallo yadda aka bibiye
sa har aka san yana da alaka dasu, ko da kuma ta hanyar nuna Bilya ya bibiye sa ne tunda an nuna shi a jami’in farin kaya. Haka kuma bai dace jami’an tsaro su tsaya tuhumar
‘yan daba a wajen ba, ya dace su tafi dasu kai Tsaye zuwa ofishin su kafin su tuhumesu akan abinda suke so su sani a can.

6- Shin wane irin hukunci hukuma ta yanke wa Ubale? Duk da irin kisan gilla tare da garkuwa da mutane da aka nuna yayi, amma bayan an
kama shi ko a fuskar shi ba’a ga nadamar abinda ya aikata ba, kuma ba’a nuna makomar sa ba, shin yaci bulus kenan?