. Kuskurai: Shida da akai acikin Film din MAI KYAU - hausanet hausanet





Sunday, 21 October 2018

Home Kuskurai: Shida da akai acikin Film din MAI KYAU

Subscribe Our Channel





Kurakurai:
1- Lokacin da Ali Nuhu yake yiwa wani matashi aski, me kallo yaga Ali Nuhu ya juya yana kallon wani bangare cikin mamaki, wanda dalilin hakan yasa matashin da ake yiwa aski ya kama fada yana nuna bai dace Ali Nuhu ya dinga kallon macen da ta wuce ba. Shin ya akayi shi matashin da ake yiwa askin ya gane cewar mace Ali Nuhu yake kallo? Ya dace a nuna cewar matashin ya juya ya kalli wajen kafin yayi furucin bakin sa. Haka kuma shima me kallo bai ga abinda shi mai askin yake kallo ba wanda ya
bashi mamaki, ya dace a nunawa me kallo ma abinda me askin yake kallo don tabbatar da maganar su.

2- An nuna wa me kallo cewa Bilkisu babbar yarinya ce wadda samari ke zubawa kudi har kusan miliyan daya a cikin account din ta, amma
sai gashi har film din ya kare da jakar hannu kala daya ake ganin ta da ita, ya dace ace duk kayan
da za’a ga ta saka to a nuna ta dauki jakar ratayawar da ta dace da kalar kayan jikin ta, amma ba wai a yi ta ganin ta da jaka kala daya ba.

3- Lokacin da Bilkisu tayi aure aka kaita gidan mijin ta, yanayin fuskar gidan da aka nuna yafi kama da wani babban hotel din ba gida ba.

4- Bayan an kori Nadiya da mahaifiyar ta daga gidan da suke haya a sanda me gidan ya mutu,
shin ina mahaifiyar Nadiya take kuma meye makomar ta a labarin? Tunda an nuna wa me kallo cewa mahaifiyar Nadiya macece mai son
abin duniya gami da wulakanta mijin ta, to ya dace a nuna wa me kallo makomar ta ko kuma a fadi yadda karshen ta ya kasance ko da baki ne.

5- An nuna cewa Nadiya tayi cikin shege, amma ba a nuna makomar juna biyun da ta samu din
ba. Shin ta haihu ne ko kuma zubar da juna biyun aka yi? Ya dace a fadi yadda karshen juna biyun nata ya kasance.

6- An samu discontinuity a lokacin da Bilkisu taje wajen almajira Nadiya ta ba ta labarin rayuwar ta, jakar hannun Bilkisu ruwan goro ce mai
turuwa, amma lokacin da ta dawo gida da bakin shuni a fuskar ta sai aka ganta rike da jaka ruwan goro me haske.

7- An nuna wanda zai auri Bilkisu a matsayin talaka futuk me sana’ar yiwa mutane aski, amma bayan auren sa da Bilkisu sai mai kallo ya gan shi a katafaren gida cikin daula wanda har wadanda suka kai amarya dakin ta suma suke mamakin faruwar hakan. Shin dama mutumin da ya aure ta din attajirin me kudi ne ba talaka ba?

Idan kuma dama mai kudi ne wanda ya boye gaskiyar matsayin sa, to ya dace a yi bayanin yadda hakan ta kasance don a fahimtar da me
kallo kuma a fidda shi daga cikin wasu-wasi.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya tafi kai tsaye bai karye ba, sai dai kuma bai dace a nuna wa me kallo cewa duk wata mace kyakykyawa tana cikin bala’i ba, domin a kowace irin al’umma akan samu mutum na gari ba batacce kadai ba, ba zai taba yiwu wa ace duk wasu mata masu
kyau a duniya halayyar su ta zamo iri daya da kyawawan matan da akayi bayani a cikin fim din nan ba. Wallahu a’alamu!