AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
Dedicated to
Hauwa A usaman
Jiddar
Kainuwa writers association
Page 104
Jin furuncin zeenat dake shiga cikin kunneta yasa tasoma yin Kasa kasa daga jikin deeni kadan ya rage bata zame ba yayi sautin tarota Amman ki yarda ta tsaya bisa kafafunta dole tasa,shima ya bita yana sake rungumeta ajikinshi
yaranta gabadaya suka sake yowa kanta suka kamkameta suna kuka .
ummi najin abinda zeenat ke faman fada tana kuruwa da zunduma ihu..... gabanta ya yanke yayi wani irin mummunar faduwa ta karasa fitowa waje da saurin maseefa.wanda har hankalin jama'ar dake cikin estate din yafara yowa kansu dan wasu daga cikinsu MA har Sun fara lekowa ta balcony suna kallonsu.
Idanun ummi suka sauka akan deeni dake durkushe rungume da nablah ajikinshi ....
kallo daya zaka masa Kasan hankalinsa a matukar tashe yake .
Sanann km take zaka gane yana cikin tsaka ME wuya.
ahankali ya dago rikitattun idanunshi ya zubawa ummi yana kallon da mamaki A saman fuskarshi .
suka hada ido da ummi wace yanayinTa kawai mutun zai kalla ya gane irin kallar tashin hankalin datake ciki.
Kallonta yacigaba dayi yana zafi cikin zuciyatsa da gangar jikinsa Wato Tana kallon zeenat ke shirin Yi masa aika aika agida batare data ta tsawarta mata ba ....
ya runtse rikitattun idanunshi yana me jin tsantsar takaicin abinda umminsa kema masa ahalin yanzu..
dakewa kawai ummi tayi tamkar bataji duk abinda ke faruwa ba tare da Nemo jarumta ta sanyawa jikinta ta dauke idanunta akan deeni kana muryarta na shaking tace zee..zeenat lafiya meke faruwa ne?
A haukace muryar zeenat na rawa jikinta na wani irin tsuma tace ummi wannan yarinyace ta km yin ciki a gidan nan har na tsawon wata shida ummi idan da ance kb NE to yanzu cikin uban waye ajikinta ? Tunda dai kb yabar gidan nan.....
banda kuka babu abinda nablah da yaranta ke faman yi .
yaran kuwa sai faman tsallara kuka suke ganin uwar su afrigice tana kuka yayinda deeni dake rungume daita yasake kamkameta tsam ajikinsa yana shafa bayanta da tafin hannushi gabadaya ji yayi sararin samaniyya da inda yake durkushe na jujjuyawa dashi.yarasa wace irin masseefa da tashin hankali ke tattare da zeenat ....
Yarasa wani irin kishin hauka gareta .
sanadinta yarasa abubuwa dayawa. Yarasa kulawar mahaifiyarsa da soyayyarta yarasa farincikinsa yarasa jin dadin duniya duk wani farincikinsa kokari take taga tadagushe masa . yayinda kwata kwata batada wani amfani agareshi yarasa abinda take nufi dashin ? Farincikinsa ta haifa masa ya'ya takasa wanda yasamu km tana neman ganin bynsu tare da sabautasu ummi na zaune tana kallo ta daure mata Gindi .
yaya ake son yayi darayuwarsa ?
Tsuma kawai yake jikinsa na kirrrma yana jin tamkar ya Mike ya sabauta mata jiki da mahaukacin duka ko zai ragewa kanshi takaicinta....
itako nablah gabanta ne ya sake yin wani irin matsanancin faduwa da karfi .
Wani irin bugawa kirjinta keyi da sauri da sauri yayinda zuciyarta ke suya da harbawa...ganin kuka bazai fishsheta ba yasa ta tasaka iyakacin karfinta ta fexge jikinta daga jikin deeni .......
jikinta na kirrrrrma ta dubi zeenat ta furta kalmar ciki.
Ciki fa kika aunty ? Meye hadina da ciki km ahalin yanzu?
takarasa mgnr tana kuka ta girgiza Kai.
Eh munafukar Allah ciki ne dake km wallahi sai Kin sanar Dani uban da dayake dirka miki ciki a gidan nan batare da saninmu ba .
deeni ya Mike tsaye da kyar jikinsa a sanyaye Tare da cire long sleeve din dake sanye ajikinshi ya sanyawa nablah.
har ya saka mata rigar hankalinta bai jikinta burinta kawai taji duk abinda ke fitowa daga bakin zeenat yazamto karyane ba gaskiya ba.ya tareta sosai da fadadden kirjinshi ta yadda bbu me ganinta kana
yasoma aikawa escort dinsa da derebobinsa da securities din da suka dan taso domin ganin tashin hankalin dake faruwa.
da wani irin kallon kasa kasa me kama da tsayuwar uwar me suke masa agurin tare da nuna musu hanyar biiiiiiii da yatsansa ...... dan kwata kwata takaicin wulakancin abinda zeenat tayi masa ya hanasa furta daidai da kalma daya ce .......
aiko take suka juya gabadayansu km bbu wanda ya sake juyowa acikinsu..
hankali nablah a matukar Tashe ta nufi
Gurin wannan takardar da zeenat ta jefar ta dauka jikinta na kirrrrma Tasoma karantawa tabbas sunanta ne rubuce cikin farar takardar dauke da ciki har na tsawon 6 months.
innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai nablah ke maimaitawa ta juyo da sauri tana duban deeni dake tsaye still yana kareta daita da jikinshi.. tsuru tayi masa da ido kawai tana kallonsa hawaye na tsiyaya daga idanunta kafin daga baya ta juya tana kallon zeenta da ummi wasu tsiraran hawaye Masu dumi suka shiga kokuwar biyo kuncinta ta dawo tamkar wata mutun mutumi atsaye a gurin.
ahankali km ta daga idanunta sama Tana kallon sararin samaniya alamun son tuno wani abu dangane da rayuwarta .. sai lokacin komai ya dawo mata.... tashiga tunani tabbas last three weeks tayi zazzabi km deeni ne yakaita hospital da kanshi byn Sun fito take tambayarshi abinda doctor yace ke damunta. yace mata babu komai malaria ce.
Wani irin mahaukacin kuka ta saki tayi jefa itama da takarda hannuta tare da daura hannuta duka bisa kanta tana ihu da kururuwa tace wayyo Allah wayyo ni nabeelah na shiga uku ni km wannan itace *K'ADDARA TAH na hauwa A usman jiddarh* sosai nablah ke kuka tana dubansu yayinda yaran suma ke Kara volume din kukansu abin gwaninsu ban tausayi. Deeni ya matso inda take tsaye tana zai ta bata tayi saurin gocewa karkar tabani .....ta dakatar dashi afrigice gashin kanta dake xube abayanta suka hargitse ta dawo tamkar wata zautauciyar makauciya . ita kuka yaran kuka. Ummi km sai rawar jiki take tana kiran sunan zeenat... Zeenat mushiga cikin gida meyasa kika Yi hk?
Meyasa baki gayamin ba...Kalli yadda idanun mutane ke kanmu.
Itama zeenat kuka take sosai tana girgizawa ummi Kai domin zuwa lokacin gabadaya jikinta da brain dinta ya gama bata yaran da km cikin dake jikin nablah na mijinta ne.
tabbas ta cuci kanta da kanta ta illata rayuwarta da rayuwar aurenta sai a lokacin abubuwa da dama suka shiga dawo mata daki daki tundaga muguwar kamar da yaran keyi da mijinta har zuwa yadda deeni kafkaf daita da yaran .
Da lokacin dayake yin kwana biyu kawai a dakinta sauran kwana biyu din baya zuwa gurinta km baya yarda tazo masa muddin bashine yaso hkn da kanshi ba.
lallai Tacika mahaukaciya mara hankali da tunani arayuwata ....wani irin mahaukacin ihu ta km sawa tayi kan nablah gadan gadan. Zata cafkota wuyanta .
deeni yayi kukan kura ya fizgo nablah jikinsa ya rungumeta tsam tsam ajikinshi ita da yaranta.... duk wanda ya Kalli fuskar Deeni yasan yakai kolowar bacin rai da tashin hankali.
Rikitattun idanun nan nashi sunyi jawur dasu tamkar an zuba masa barkono ciki .
gaban fuskarsa sun canza suma sunyi jawur..
ba zeenat ba har ummi sai data tsorata da ganin yanayin da deeni yashiga bbu abinda yafi kona masa rai da taba zuciyarsa irin yadda zeenat ke kokarin hankada nablah waje babu kaya ajikinta ga kukan da yaran ke faman Yi fuskarsu tayi ja. Nablah na rungume ajikinsa da yaran ya nufi hanyar cikin gidan dasu zeenat tayi saurin tare hanyar tana jifansa da wani irin matsiyacin kallon....
Muryarta a matukar hassale tace bafa zata km taka kafarta da sunan shiga gidan nan ba.
Ummi tayi saurin janye zeenat da iyakancin karfinta daga bakin kofar Sbd ganin yadda deeni ke aikomata da kallon tashiga cikin hankalinta dashi . Tasan shi , tasan halinsa, tasan tashin hankalin dake saurin haukatashi da wuri har ya autsina tunaninsa.. Yasa gabadaya arasa gane kanshi..
Ahankali yasoma takawa zuwa cikin gidan nablah na rabe da jikinsa suka shiga cikin parlour 'n .
ahankali ya zaunar daita akan kujera zuciyarsa na dokawa ya zauna yana facing dinta tare da tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa... yayinda kaunarta ke sake karuwa acikin zuciyarsa Tare da bin kowane part na jikinsa....tsawon lokaci yana zaune yana kallonta yarasa takamaimain abinda zai ce mata..
kukan kura zeenat tayi,tashigo cikin parlour 'n bata tsaya wata wata ba tayi kan nablah ta shako wuyanta ta hada da yaran ta janyosu...... yaran suka sake sakin wata uwar kara duk suka frigice cikin kuka tace wlh baki isa kiyi Zina kina yin cikin shege kina kawo min gida ba .
mazinaciyar banza kawai gyaran muryar deeni yayi yana kallon tsaitin da ummi ke tsaye tana rawar jiki alamun tayi wani Abu akan haukan da zeenat keyi Amman sam ummi takasa aikata komai gabadaya tsaye kawai take bisa kafafunta komai yagama cakude mata waje daya Dan kusan duk ummi tafi kowa tsurewa da shiga tashin hankali Mara misaltuwa banda rawa babu abinda Jikinta keyi takasa tabuka komai .
Baka jin komai a parlour'n sai hargagin ihun zeenat wallahi sai Sun bar min gidana daga ita har wadan nan shegun yaran tsinannu tabbbbbbbbb wani irin yunkurawa deeni yayi a matukar fusace ya janyo zeenat yayi wurgi daita gefe daya yana aika mata da wani irin kallo da jajayen idanunshi dasuka gama rikedewa suka canza kala yana fidda wani irin numfashin tamkr wani zaki .....
Zumbar zeenat ta Mike tsaye tana dubansa ranta abace ta nuna inda nablah ke tsaye da yatsansa hannunta Kana tace akan wannan yar iskar karuwar Kake son wulakantani da nunawa duniya ni din bawata tsiya bace agurinka?
A harzuke muryasa na rawa jikinsa na tsuma yace karki sake ce mata Karuwa...... ummi tayi tsalle takaraso gareshi ta katse shi ta hanyar ce masa karka sake kace komai deeni. ......ban baka umarnin cewa komi ba deeni....
a fusace yajuyo zuciyarsa na dokawa da sauri yace enough is enough ummi ....the game is over Now & nobody will stop me to tell the truth ....ba karuwa bace ya fuskanci zeenat da kyau kirjinshi na wani irin bugawa *MATATA CE* Ta sunnah kmr yadda kike matata. yadda kike agurina haka take agurina koma ince har tafiki........ jikin ummi ya tsananta rawa kar karrr ta koma ta zauna jagwab kan kujerar mutun daya hade da dafe kanta ta hannuwanta duka tana kuka sharrrrr sharrrrr.
yayinda shi km deeni yacigaba da facing din zeenat yana mgn ransa a matukar bace... wayan nan ya'ya dakike ganin *haidar* *Anan da *junior* duk ya'yanane na halak malak Wanda ko yanzu inda babu ni a duniya sune magadana sannan uwarsu tana da kima da mutunci a idanuna Wanda har duniya tane bazan daina ganinta da wannan darajar ba .
ita da mahafinta wanda shine ya Aura min ita batare da sanin koni waye ba da matsayin dana taka a fadin duniyar nan sannan da kafafuna na taka har zuwa gurin mahaifinta na roki aurenta agurinsa km ya amincemin ya Aura Min ita.
ummi tun haihuwar yaran nan yakamata ace an fito da sirrin boye....amman nake ta mike biyayya ummi zaki Kaini wuta km babu biyayya gurin sabawa ubangiji ga abokin halitarsa nablah *Mamata ce* kmr yadda zeenat take Matata gabadayansu daya ne agurina....babu wani bambamci.. bansan meyasa kike son tauye Hakin nablah akan zeenat ba....Wani irin gigitaccen ihu zeenat tasaka ta fixge dan kwalin kanta dayagama karkacewa tayi cilli dashi gefe tana karkada gashin kanta.. wallahi wallahi baka isa ba *DEENI* wannan zance banza ne da daji ma ansan karyar ne wlh ta ina haka zata kasance kace dai kabi dare kabi duhu ka dirkawa wannan yar iskar karuwar ciki Amman ba dai wani aure ba wlh.. Ta zabura ta dauki glass cup din dake ajiye a saman center table ta cilawa nablah dake tsaye wace jinta da ganinta ya dauke sai idanunta dake tsaye kyam akan deeni .Tana kallonsa..
Deeni yayi saurin cafke glass cup din..tacigaba da ihu tana kururuwa wlh wlh karya ne wannan abar tazama kishiyata .
amatukar razane takira Sunan ummi da karfin gaske ...ummi... ummi kina jin abinda yake cewa wanda ni nasan karya ne hakan baxai taba faruwa ba agidana.
Kishiya a gidana never in history tanakarasa fadar hk tayi hanyar kitchen da gudu.. ummi ta zabura ta Mike tsaye tabi bynta da gudu itama tana kiran sunanta. wanda sai lokacin nablah ta dawo cikin natsuwarta da kyau sannan km farat wani matsanamcin tsoro yashigeta jikinta yakama rawa ta rude tana neman hanyar tsira ..
ummi ta kwalla kara ta biyo zeenat tana kokarin kwace wukar hannuta Amman ina takasa tana fitowa nablah ta saki Kara itama wanda ya sake frigita yaran sukayo gurinta tare da rungumeta... deeni ya tsurawa zeena ido yana kallonta rike da wuka sannan kausashe yace meyye hk ko kina hauka ne?
Kai ne dai mahaukaci tunda gashin nan brain dinka ya juye kana fadar abinda bazai taba yiwu ba.
ke kuwa zaki ci kashi binshin kutumar ubanki yau ta nuna tsatin cikin nablah da wukar
Jikinta na wani irin tsuma. Wallahi yau sai kinga kudi kince kashine dan bazan barki ba sai naga bayanki gobe ma bazaki km zama karuwar wani ba MA ba mijina ba.zeenat zan mugun saba miki zan shuka miki ranshin mutunci zan baki mamaki wlh idan kika km cema yarinyar nan karuwa .
ummi kina ji kina gani kiyi Mata mgn zan canzawa zeenat kamanin wlh idan bata gyara furuncinta bakinta akan yarinyar nan ba haba wannan irin maseefa ce hk ba aure na aureta.?dan ita kadai Allah ya haliceni?
jikin Ummi na tsuma tace yiwa hakuri karka mata komai dan girman Allah. Allah Yayi maka albarka... Ya tabe baki kawai yana kallonsu yana girgiza kai.
Nablah tayi tsuru tsuru tana kallonta atsorace sannan muryata a raunane tace please aunty ki kiyi hakuri ki dawo cikin haiyaciki dan Allah ta yaya ma zaa yi mijinki ya zama nawa wlh ba mijina bane km Nisan Allah duk abinda ya fada miki karyane ba gskiya bane kutumar ubanki ina mgn kina maidamin.
da mijina nake mgn badake bakar Karya munafuka maciya amana ta nufota ummi ta Saki kara tana kuka yau ME zangani ni fadeela Dan girman Allah zeenat ki ajiye wukar nan kada kiyi kisa kisa zuciyata ta buga.. Kada Allah yasa ta ajiye wukar ummi tana ganin idan ta illata yar mutane zaa kwaleta ne .
wlh da kaina zan hada da hukuma ahukuntata yarinyar nan Matata ce fine banga wani abun boye boye aciki ba ummi .
Muryar nabla na shake tace dan Allah mlm ka daina cewa matakar ceni. wannan ma ai rainin hankaline tayaya ma hkn Zai kasance?
. Ta yadda ya'yanki ke Kama Dani kadai ya isa yasa ki fahimce komai km kisan hakan ma yagama kasancewa inji cewar deeni ya fada yana watsa mata kallon rainin hankali . Ko ki yarda ko karki yarda ni mijinkine km uban ya'yanki.
Zeenat tace Karyane bazata taba zama matarka ba sai dai Karu...ya daga hannu zai sauke mata wani gigitaccen Mari ummi ta katseshi ta hanyar buga masa tsawa kamin shr dan ubanka km wlh karka sake kataba min lfyr yarinyar da ME zataji?
da wannan maseefar data kunno Kai ko me? Wlh idan kayi sanadiyar da zeenat dina tashiga cikin wani Hali ko wani Abu yasameta nima bazan yarda ba.
ummi kinsani nasani nablah Matata ce ta sunan wace kece silar komai to meyasa kike nuna kmr bakisan komai ba ? Kodan banida gata bani kowa komai sai ki dinga nuna son kai akan zeenat........
Jin hk yasa zeenat yin cilli da wukar hannuta tare da ja da baya dafe da tsaitin zuciyarta tana kallon ummi wasu sabbin hawaye na tsiyayo mata bisa kuncinta ummi tarasa yadda zatayi da rayuwarta.. kawai tashiga girgizawa zeenat Kai zeenat ta zubara ta Kalli deeni muryarta na rawa cike da in.. Inna tace karya ne wlh badai ummina ba ummina bazata min hk ba ...Kai ban ma yarda kayi wani aure ba ..nasan ko aure zakayi bazaka taba auran wannan yarinyar ba yar talakawa kaskantaciya Mara galihu wace tazo aikata domin Rashi da talauci ... ummi ta fashe da kuka tana kokarin Kamo hanun zeenat cikin nata.
deeni ya rigata ya damki hannun zeenat cikin nashi ya nufi hanyar step daita ta tokare taki mov ka sake maci amana wlh sai Allah yasaka min nasoka arayuwata. Numfashina ne kawai bazan iya fixge shi nabaka ba Amman karasa sakayar da Zaka min sai wannan tana kuka takarasa mgnrta tare da son fixge hannuta daga nashi Amman takasa sbd bakaramin riko yayi mata ba. Bai daita komai ba kawai Cigaba da tafiya yayi da ita har yayi taku uku ya Dan tsayawa ya juyo yace nablah ta biyoshi itama.
Da sauri ta girgiza masa kanta alamun bata zuwa tasoma neman hanyar guduwa batare yaranta ba.
Ya dawo ahankali ransa a bace ya kule Duka kofofin parlour gabadaya wanda zasu sada mutun zuwa waje gudun kada nablah ta gudu .
sannan ya nufi dakinsa da zeenat itama sbd tsaro ya tafi daita dan yasan kafin yaje ya dawo ta illata nablah. ya je ya dauko wayarsa wanda akayi video dauren aurensa da nablah ya dawo parlour km duk lokacin still zeenat na rike cikin hannushi gam jikinsa a sanyaye ya hada wayar da makeken TV dake manne da jikin bangon parlour'n ya tsaita komai ya kunna gabadaya daga zeenat har nablah babu wace kirjinta bai buga ba Dan tsabar frigicin abinda zai biyo baya.
gabadaya idanunsu nakan TV yayinda zuciyar ummi ta dinga tsalle tana tafarfasa jikinta na rawa rawa tana juya Kai tana uhmmmmm uhmmmmm deeni karkayi hk please tayo inda TV yake da niyyar kashewa Amman ina aikin gama ya rigada ya gama dan Kafin ta karaso har mutanen ciki sun soma bayyana .
cak taja tsaya tana salallami da ambato Sunan Allah gabadaya babu inda bai dauki rawa ba ajikinta .
daga zeenat har da nablah zuciyoyinsu ke bugawa tmkr ana buga musu guduma.
deeni kuwa kamo yaransa yayi ya zaunar dasu sai faman ajiyar zuciya suke ja suna fitarwa tsabar kukan da sukayi gabadayansu suka kwanto jikinsa . Sosai nablah ke kallon mahaifinta yana murmurshi tare da wasu daga cikin makwatansu na uguwarsu Take jikinta ya dauki wani irin rawa karrrr..... karrrrr ....karrrr ta sake kurawa TV idanuta tana kallon komai azahirance.
A matukar frigice itama zeenat ke kallon tsirarrun mutane dake zaune suna gabatar da daurin aure har sanda taji an ambaci sunan mijinta km an daura auren dashi Tana Gama jin hk ta saki wata razananniyar kara wanda gabadaya gidan ya amsa tare da zubewa kasa sumammiya....................
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.