. BAMBANCIN SOYAYYA DA KUMA SHA'AWA - hausanet hausanet





Tuesday, 23 October 2018

Home BAMBANCIN SOYAYYA DA KUMA SHA'AWA

Subscribe Our Channel


:BAMBANCIN  SOYAYYA DA KUMA SHA'AWA

Idan soyayya ta tsaya a kan kula da juna ta bangaren abin sakawa a bakin salati, ko matsuguni, ko sutura, ba shakka dabbobi da tsuntsaye ga wanda yake lura da rayuwarsu suna yin sama da abin da mu mutane muke yi, hatta ta bangaren saduwa da qoqarin biyan buqatar juna a matsayin ma'aurata kuma masoya, ga qaramin taqadiri nan zakoki, birai, tantabaru da giwaye, Allah SW ya bambanta mu da sauran dabbobi ta fuskoki daban-daban.

Dan adam shi yake tunanin wa zai nema? Ya dabi'un wanda zai nema suke? Ya aqidu da tarbiyarta? Ya iyayenta suke? Sannan ya yi tunanin irin 'ya'yan da za ta haifa da irin tarbiyar da za ta ba su, shi ne  yake tunanin cewa aurennan fa ibada ne, kuma lada zai samu idan har ya yi, ya riqi surukai a matsayin iyaye, ya je zance gidansu yarinya yadda iyayenta za su kalli dabi'unsa su tantance shi, su tabbatar da cewa lalle ya isa ya zama uban jikokinsu.

Kafin a fara tunanin wasu hidundumu na sanayya da al'adu wadan da za su tabbatar wa iyayen yarinya cewa tabbas yaronsu zai iya riqe diyarsu, ta fuskar mu'amalla da zamantakewa? To idan ba zai zo ba sai da daddare, kuma daga shi sai ita, sannan a can waje yadda ba wanda zai san abin da suke qullawa _tabbas an yi kuskure wajen fassara ma'anar soyayya,_ ina da tabbacin in kishi da kula da manne wa juna su ne soyayya, to ba 'yan adam ne kadai suke yi ba, kuma dabbobi sun fi mu iyawa, don kuwa ba sa yi sai sun yi shaquwar aure, mu kuwa kafin aure ne namu yake da qarfi, bayan aure kuwa kuma sai zaman haquri da juna.

*Tambaya* : Don me aka halicci ma ce? Don ta yi gogayya da namiji a matsayin abokiyar halitta? A'a, don ta zama wa namiji ne ruwa mai kashe wutar sha'awa da kadaituwa, da rigingimun waje, wadan da suke damunsa a zucuyarsa, ta yi masa magana mai dadi da Allah ya siranta ma ta dominsa, ya raunana duk wasu gabobinta yadda za ta iya yi masa hidima, ya sanya murnarsa da farin cikinsa a hannunta, ya mallaka ma ta zuciyarsa yadda ko'ina ya je tunaninsa yananan tare da ita, kullum qulaficinsa da hanqoronsa kawai shi ne ya kare ta da mutuncinta, ya zama ma ta komai har ta manta da iyayen da suka haife ta ma, in don hidima ne ba don uwayantaka ba, duk in abin farin ciki ya taso sai a tuna masoyi, haka in na baqin ciki ya taso masoyi ne farkon wanda yake fadowa a rai nikan  na tabbata hakane.

Da yawa mata da 'yammata suna jahiltar dalilin da ya sa Allah SW yahalarci mace, a haqiqa Allah ya halicce ta ne don ta yi soyayya ta wajen ba wa maigidanta damar samun natsuwa a wurinta, ga ma aya nan Allah SW yana gaya mana dalilin halittar mace:-

(Daga cikin ayoyinSa ne Ya halitta muku mata daga jikinku domin ku sami natsuwa a wurinsu, Ya sanya qauna da tausayi a tsakaninku, haqiqa akwai ayoyi a kan wannan ga mutanen da suke da tunani).🧠
*08134928733*

Mace dai mutum ce mai daraja kamar kowani namiji, an halicce ta ne daga namiji, tana dauke da daidaituwar karamci da tausayi da tausasawa, ba wani abu da Allah SW ya yi ma ta sai ka gan sa kyakkyawa; Murya, fuska, tafiya, ado da kwalliya, matsayinta a wurin wadan da suka san darajarta babba ne, don ita ce asalin duk wani alkhairi, wasu can da suka rayu nesa da muslunci sun riqa yin jayayya a tsakaninsu ko mace mutum ce kamar kowa, don wasu suna ganin dabba ce maras matsayi a tsakaninsu. 08134928733

Mu kam a muslunce MACE MUTUM CE, Allah SW ya halicce ta ne da sura ta dan adamtaka, ta wajen tsari da siffa, har ma kuma tsarin halittarsa ya fi ma na namijin, ta yadda zai buqace ta don ya gama kammaluwa a matsayinsa na mutum, ta ba shi natsuwa da farin ciki, ta zama masa rumbun killace dukkannin asiransa, kuma ministan harkokin cikin gidansa, mai ba da shawara game da alaqoqinsa na waje, masamman abubuwan da suka shafi 'yan uwansa da zumuntarsa, irin wadannan abubuwa ba su da alaqa da *sha'awar saduwa  kamar yadda dabbobi suke yi, abubuwa ne da suke daure zuciyoyin aminai su sanya su begen juna in an rabu, ko qaunar juna in ana tare.

Mun sha gani ba sau daya ba, ba sau biyu ba, inda wani baqi dan Arewa yake zuwa kudu ya auro farar mace, wace ta sa6a masa a al'ada, addini, abinci da tufafin sanyawa, amma da zarar ta zo gidansa sai ta mai da iyayensa na ta, ta fara koyon harshensa, ta yi kyakkyawan shirin hayayyafa masa yadda za ta daure kanta da shi, har dai ta kai inda ba ta da sauran natsuwa in ya fita har sai ya dawo, qoqarinta dai ta gan sa a gabanta, yana dawowa ta tarbo shi cikin farin ciki da jin dadi kamar wace ta yi shekaru ba ta gan sa ba, wannan ita ce soyayya ba sha'awa ba. Matan arewa kuyi hkr don Allah bana nufin cin fuska a gareku amma gaskia kuna banbanta da sauran mata na sauran wurare. Irin addinin mu suke yi

Zamu ci gaba insha Allah.saga www.hausanet.ml