Zuciyarkita zama takarda, tawa ta zama bir in rubata miki shafin kauna Kizama kofa na Zano makulli, mu hadu mu bude kofar soyayyyar lambun zuciyata! Na kasa tsaye na
kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban kaman wata daren sha biyar!
Ya madarar zuciyata, ki zamo ciminti in zamo bulo mu gina gidan
Quana a filin soyayya.Watau yau da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske nan din nan amma duk haskenta ba kai hasken fuskar
da haske zuciyata,domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk hasken raina Ki zama petur na zama inji mu hadu
mutaa da lantarkin qaunaya shiba ta na baki filin zuciyata ki shuka aduk wani lungun da sako bushiyar so a kauna don mu sami
inuwar da zamu zaunamuyi soyayya.
Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwata bake
tamkr lami ce ya rabin raina
Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na sha za ta
haska ka zuciyata ta yi fari.
Rayuwata babu ke tamkar wayar da chaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.Kunne ya kur mance saboda rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai
dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum.Ta tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda
rashinganinki a yau da kullumYa gangariyar madarar zumar da batada gauraye, ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske
zuciyar masoyinta. Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya don ya gan ki. Ziciyata na shan lagwadar zuma da madarar kaunaIdon
basira lafazin rayuwata
Alfijirna quana ya keto, tsuntsayen soyayya sun tashi su na
yayo a sararin samaniyar zuciyata Ya fankar da ke juya zuciyata, zan zamo kwale kwale
ki shigo bu haukan kogin so, in zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin kauna.Hadarin begen ki ya hado, guguwar sonki ta taso, sai
ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki afilin zuciyata.Gaisuwa daga kamfanin so, harabar
kauna,gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwaga rabin rayuwata.ya zare da allurar da ta dinken zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a
nijeriya. ya majaujawar zuciya ta, zan zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin
rijiyar soyayya. Ya tsokar zuciya ta, zan so ace ki zama furain zama nono mu hadu a kwaryar soyayya.Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya.Ya masoyiyata ki zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar
da ke.Ya masoyiyata, ki zamo hanta
inzamo jini, muga mai raba mu. Ludayin kaunar ki
ya mamaye min kokon zuciyata.Ya
masoyiyata ki zamo mai in zamo albasa mu hadu mu
soye juna.'.ya masoyiyata, ki zama candir in zamo ashana, ki zamo itace in zamo makamashi mu hadu mu hura wutar so, domin mu mutafasa tukunyar kauna Kixama aruma naxama Sadauki mu hadu mu yaki duk wani makiyin soyayyan mu daga naku baban soyayya namalika
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.