. KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA - hausanet hausanet





Friday, 25 May 2018

Home KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA

Subscribe Our Channel


ANNURIN
RAINA JIGON RAYUWA NA QUEEN
FATIMA ZAHRA da kyalli a cikin zuciyata ba zan iya rayuwa daidai da minti dayaba ba tare da ke ba
saboda kece kadai a rayuwata ina sonki Ina kaunar ki gimbiya ta kece masoyiyata ta hakika a cikin wan nan duniyar, ina sonki na ne har abada ko alama ba zan iya mantawa da keba saboda cigaba da kaunarki abune mara gushewa ina sonkine
fiye da yadda nake son kaina ina sonki ne fiye da yadda kike tunani ina sonki san nan kuma a shirye nake da na mutu a kanki bani da wani abuda zan tuna a koda yau
she fiye da ke kowane irin ma tsayi zan fuskanta a rayuwata koyaya
jama’a zasu tsaneni, yake zuman raina koda me mutane zasu kirani

To kuwa zan kara farashin soyayyata a gareki zan cigaba da sonki. Kuma zan nuna miki soyayyata a gareki
tsarkakakkiya ce. nayi imani cewa soyayyarmu ta hakikace ba a binda zai sanya in daina sonki har a bada komai tsa nani komai wuya Queen Fatima zahra na kece farin cikina hakika ba rayuwa gareni idan bakya
kusadani duk na damu yaxanyi da rayuwata jinina ya riga ya gaurayu da naki Ilove you Queen fatima
zahrat shi da soyayyar dake cikin zuciyar Mace. Soyayyar Mace
Idan har kaine wanda zuciyarta ta aminta da ita, kuma tana sonka–Ina nufin so na hakika?–Ita ce zata rinka
kakkabe ka idan kayi kura, zata rinka
kareka ko tana tunanin kaine baka da gaskiya, sannan zata aminta da
dukkan kalamanka ko da kuwa kullum karya ce kake shirya Mata. Bazata damu da dukkan abubuwan da kake mata ba, bazata damu da cewar kawayenta kullum na fadi
mata Wannan bai cancanta ba bazata damu da adadin lokutan da kake kokarin katse dukkan wata
alaka a tsakanin ku ba, zata kasance tana iya bakin kokarinta tare da mallaka maka dukkan zuciyarta, kuma kullum kokarinta ya zamana ta mallaki taka zuciyar koda kuwa kai kana daukarta a matsayin Wacce ko me zata yi bata kai masayin ka bata zuciyarka ba

Wannan fa itace Soyayyar Mace Tana zama ne na tsawan lokaci, cikin yarda da kuma sadaukarwa a ko wane hali Babbar matsalar a nan shine, Burin su Namiji ya rinka yi
masu irin wannan Son. Ka tsaya ka tambayi ko wace maceIna nufin ko wace ce, shin ya take so wanda take
so ya Sota, da yanayin yadda take so ya kasance Amsarta zata kasance kamar haka Ina so ya kasance mai nustuwa da dattako, mai son wasa da kuma iya soyayya, mai saurin
fahimya kuma wayayye, mai son addini ga wasu ke nan sannan abinda yafi dukkan su, ya zamo mai bani kulawa a ko wane lokaci. Ina son wanda zai kakki kwayar ido na ya fadi min ina da kyau kuma na yi mashi. Ina son namiji mai juriya
idan na bata mashi rai ko wani ya bata mashi, wanda zai kawo iyayen shi don kulla zumunci da nawa, wanda ke son Yara, wanda zai rinka taya ni gyaran gida da wanke wanke ba tare da na ce yayi ba. Sannan
idan yana da kyau da fasalin jiki kuma yana da kudi masu yawa, yana da tarin kadarori. To irin haka zan so ya so ni Ameen To ‘yar uwata kanwata, yayata, diyata, ko kuma tamkar uwata, ina so in sanar maki cewatunanin samun irin

Wannan soyayyar da dukkan yanayin
shigaskiya abune mai matukar wuya. Maganar gaskiya ke nan. Zan kara mai maita maki—hakan bazata taba faruwa ba ba tsumi babu dubara. Saboda ita soyayyar Namiji a cikin
zuciyat shi ba wai irin soyayyar dake cikin zuciyar Mace ba ce Ka ki rikitar da kanki, ki fahimce ni—ba wai ina cewa ko maza basu iya yin hakan ba, ko basu da cikakkar zuciyar da zasu so ki so tsantsa, a’a. Ni kawai abinda nike so ki fahimta shine ita soyayyar Namiji daban ce tana da sauki
a wajen shi, ba wani dogon tunani mai wahalar da zuciyar shi, sannan zan iya cewa zata iya zama da
yanayin wuya kafin ya saba da ita.
Bari dai na d’an yi maki karin bayani: Namiji idan yace yana sonki bawai zaki sa ranki zai rinka kiranki a waya duk bayan rabin awa ba don sanar dake yadda sonki ya karu karfe 5:30 na safe ba kamar yadda yake
sonki da karfe 5:00, mintuna talatin da suka wuce bazai zauna kullum a
kusa dake idan mijin ki ne yana gyara maki gashinki ko yana tayaki tsifa ba Ita soyayyar shi kawai

Soyayya ce, ku,a kiyi tunani. Kawai banbanci ne tsakanin soyayyar da
mace kewa namiji da irin wacce take samu daga gare shi. Musamman yadda na fahimta cewa, mata sun fi son abinda zuciyar su ta kawata masu akan namiji amma ba namijin da ya da ce da su ba. Taya zaki yi
tsammanin zai soki yadda kike son shi Amma ya zaki gane Namiji na sonki Cikin sauki