. An kirkiro sabuwar man haja (software) dan masu neman karin aure - hausanet hausanet





Sunday, 27 May 2018

Home An kirkiro sabuwar man haja (software) dan masu neman karin aure

Subscribe Our Channel


An kaddamar da wata sabuwar
manhaja a kasar Indonesia don
masu sha'awar yi wa matansu
kishiya ta hanyar intanet Manhajar mai suna AyoPoligami wadda ta janyo takkadama a kasar wadda ta fi kowacce yawan Musulmai a fadin duniya na ba wa maza masu sha'awar kara aure neman wata mata, har ma su yi zance da wasu mazan da ke da irin wannan niyya.
Mutumin da ya kirkiro manhajar
Lindu Pranayama ya kare wannan
fasaha da cewa za ta biya dumbin
bukatun da ke akwai. Muna ganin wani al'amari inda maza masu yawan gaske ke neman kara aure, amma idan suka je shafukan hada soyayya, ba sa ganin zabin yi wa matansu kishiya Ya ce ba a yi musu tanadi don neman karin aure na biyu ko na uku ko ma na hudu

Sai dai masu fafutukar tabbatar
da daidaiton jinsi na ganin wannan
manhaja a matsayin wadda ke
tunzura auren mace fiye da daya
da kuma musguna wa mata Wata mai rajin tabbatar da daidaiton jinsi, Zakia Tunisa ta ce abin takaici ne da firgitarwa karon farko da ta ji batun wannan manhaja A cewarta kafin ma a samar da manhajar kara aure da ma auren mace fiye da daya ya yawaita Ta ce manhajar na ingiza auren mata da dama don ya samu karbuwa a tsakanin al'umma, mai yiwuwa ma kuma ya tilasta wa mata su yarda da shi tnx for visit www.hausanet.ml