. KU KOYAWA IYALANKU TAUHIDI TA HANYAR YAWAN MAIMAITA MUSU TAMBAYOYIN NAN - hausanet hausanet





Monday, 28 May 2018

Home KU KOYAWA IYALANKU TAUHIDI TA HANYAR YAWAN MAIMAITA MUSU TAMBAYOYIN NAN

Subscribe Our Channel


*TAMBAYA TA 1*
A ina muke samo aqeedar mu ?
*AMSA*: a cikin Al-Qur'ani da Sunnah

*TAMBAYA TA 2*
A ina Allaah yake ??
*AMSA*: Yana sama akan Al-arshi.

*TAMBAYA TA 3*
kawo hujjah daga al-Qur'ani akan Allaah yana kan Al-arshi ?
*AMSA*: Allaah yace: (( _Allaah mai rahmah ya dai-daita akan Al-Arshi_ ))

*TAMBAYA TA 4*
Meye Ma'anar Lafazin "Ya dai-daita" ??
*AMSA*: ma'ana: Ya dauka, ya buwaya

*TAMBAYA TA 5*
Shin Allaah yana ko ina ??
*AMSA*: A'a, Allaah yana sama.

*TAMBAYA TA 6*
Saboda meye Allaah ya halicci mutum da aljani
*AMSA*: Domin su bauta masa shi kaɗai, kada su haɗa shi da komai a cikin bauta.

*TAMBAYA TA 7*
Meye dalili a cikin Al-Qur'ani akan Allaah ya halicci mutum da aljani don su bauta masa ??.
*AMSA*: Allaah yace (( _Ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini_ ))

*TAMBAYA TA 8*
Mene ne ma'anar lafazin "don su bauta min" ??
*AMSA*: Don su kaɗai ta ni a cikin bauta.

*TAMBAYA TA 9*
Mene ne ma'anar _Laa ilaaha illal Laah_ ??
*AMSA*: babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah.

*TAMBAYA TA 10*
Mene ne mafi girman Bauta
*AMSA*: Tauhidi

*TAMBAYA TA 11*
Mene ne mafi girman saɓon Allaah ??
*AMSA*: Shirka

*TAMBAYA TA 12*
Mai ake nufi da Tauhidi ??
*AMSA*: Shine kaɗaita Allaah da bauta.

*TAMBAYA TA 13*
Mene ne shirka ??
*AMSA*: bautawa wanin Allaah tare da Allaah.

*TAMBAYA TA 14*
Tauhidi ya kasu gida nawa ??
*AMSA*: ya kasu gida uku.

*TAMBAYA TA 15*
Lissafo karkasuwar Tauhidi ??
*AMSA*: -Tauhidur Rububiyyah, Tauhidul Uluhiyyah da Tauhidul Asmaa'i Was- sifaat

*TAMBAYA TA 16*
Mene ne Tauhidur Rububiyyah ??
*AMSA*: shine kaɗaita Allaah da ayyukan sa, misalin Halittawa da Azurtawa.

*TAMBAYA TA 17*
Mene ne Taihidul Uluhiyyah ??
*AMSA*: shine kadaita Allaah da ayyukan bayi. Kamar Addu'ah, yanka da sujada.

*TAMBAYA TA 18*
Shin Allaah yana da sunaye da siffofi ??
*AMSA*: Eh yana da su

*TAMBAYA TA 19*
A ina muke samo sunayen Allaah da soffofin sa ??
*AMSA*: daga Al-Qur'ani da Sunnah.

*TAMBAYA TA 20*
Shin siffofin Allaah irin siffofin mu ne ??
*AMSA*: A'a.

*TAMBAYA TA 21*
Kawo hujjah cikin al-Qur'ani akan lallai siffofin mu basuyi kama da siffofin Allaah ba ??
*AMSA*: Allaah yace: (( _Babu abinda yayi kama da shi (Allaah). Shi mai ji ne mai gani_  )).

*TAMBAYA TA 22*
A-Qur'ani maganar waye ??
*AMSA*: maganar Allaah

*TAMBAYA TA 23*
An saukar da al-Qur'ani ne ko an halicce shi ??
*AMSA*: An saukar da shi ne

*TAMBAYA TA 24*
Mene ne ma'anar Alba'ath ??
*AMSA*: raya mutane bayan sun mutu.

*TAMBAYA TA 25*
Kawo hujjah cikn al-Qur'ani akan kafircin wanda ya qaryata tatar da halittu bayan mutane.
*AMSA*: Allaah yace: (( _waɗan da suka kafirta suna tsammanin ba za'a tashe ba_ ))

*TAMBAYA TA 26*
Meye hujjah cikin al-Qur'ani akan tabbas Allaah zai tayar da mutane bayan sun mutu ??
*AMSA*: Allaah yace: (( _kace (musu) na rantse da ubangiji na sai an tashe ku_ ))

*TAMBAYA TA 27*
Rukunnan musulunci guda nawa ne ??
*AMSA*: guda biyar ne.

*TAMBAYA TA 28*
Rukunnan Imani guda nawa ne ??
*AMSA*: guda shida ne.

*TAMBAYA TA 29*
Rukunnan kyautatawa guda nawa ne ??
*AMSA*: guda daya ne.

*TAMBAYA TA 30*
Mene ne musulunci ??
*AMSA*: shine miqa wiya ga Allaah  da tauhidi. Ta jawuwa a gare shi da yi masa biyayya, da barranta daga shirka da ma'abotan ta.

*TAMBAYA TA 31*
Mene ne ma'anar imani ??
*AMSA*: shine yin imani da Allaah, da mala'ikunsa, da littafansa, da manzanninsa, da rana ta Qarshe, da Qaddara ta alkhairi da ta sharri.

*TAMBAYA TA 32*
Tayaya imani yake kasancewa
*AMSA*: imani yana kasancewa ne a zuciya, da furuci da harshe tare da aiki da gabbai. Yana ƙâruwa da aikin Kwarai, yana tawaya da sabon Allaah.

*TAMBAYA TA 33*
Shin zamu iya yin sujada ga wanin Allaah ??
*AMSA*: A'a

*TAMBAYA TA 34*
Waye ya kamata muyi masa sujada ko yanka ??
*AMSA*:  Allaah shi kadai

*TAMBAYA TA 35*
Meye hukuncin yin sujada ga wanin Allaah ??
*AMSA*: Babban Shirka ne.

*TAMBAYA TA 36*
Mai zaka ce akan Sahabbai ??
*AMSA*: Allaah ya qara musu yarda.

*TAMBAYA TA 37*
Shin ya halarta mu zagi Sahabbai ??
*AMSA*: A'a.

*TAMBAYA TA 38*
Shin muminai zasu ga Allaah a ranar alqiyama ??
*AMSA*: Eh zasu ga Allaah

*TAMBAYA TA 39*
kana son Ahlul baiti ??
*AMSA*: Eh ina son su

*TAMBAYA TA 40*
Lissafo abinda kayi imani da su a ranar alƙiyamah ??
*AMSA*: nayi imani da aljannah, wuta, siraɗi, mizani da Tafki

*TAMBAYA TA 41*
shin Annabi Isah zai dawo ?
*AMSA*: Eh zai dawo a qarshen duniya.

*TAMBAYA TA 42*
Shin manzon Allaah ya san gaibu ??
*AMSA*: A'a bai san gaibu ba.

*TAMBAYA TA 43*
Meye dalili akan haka ?
AMSA Allaah yace: (( _kace (musu) babu wanda ya san gaibu cikin ƴan sama da ƴan Qasa sai Allaah