. YADDA KUMA ZAKU HADA TURAREN HUMRA - hausanet hausanet





Thursday, 10 May 2018

Home YADDA KUMA ZAKU HADA TURAREN HUMRA

Subscribe Our Channel


Humra turare ne wanda aka samo
asalinsa daga Arabs, (Larabawa) kuma Bare-bari suka dauka a matsayin kwaikwayon al’aadar, sannan ta yadu a kasar Hausa, kusan duk mata sun karbe shi sakamakon irin ingancinsa tare da cikakken muhimmmancin sa.TurareHumra na dauke da sinadarai masu kamshi, ana
kuma hada shi ne da saiwoyi da nau’oin turarruka daban-daban, kuma ta kan zo a nau’in bakar humra ko fara har ma da koriya---->

Abubuwan da ake hada bakar Humra da su. Ruwan turare na 1.farko (Alchohol) litre 1 Madarar turare 1/6 litre *Ambir 4 (gwayar shi) Garin sandal cb 2 Garin Humra cb 3  Garin soyayyen kaninfari ck1 Mahalan (gari)ck 1/2 Yadda ake
hada bakar Humra: 1.Za’a sami ruwan turare a zuba masa nikakken ambir 2.na biyu Sai a kawo garin nikakken tankadadden sandal da garin Humra da soyayyen garin kaninfari, da garin mahalan, a zuba a hada su a girgiza, akawo madarar turare irin nau’in da ake bukata a zuba, zai iya kasancewa fiye da daya ko fiye idan sun hadu sai a
zuba a cikin kwalabar turare a rufe.
Farar Humrada Koriya Ita ba’a sa mata garin Humra, shi ne kadai babu,a cikin koriyar Humra kuma kala ake sa wa koriya, ita ma din kadan, kuma babu garin Humra a cikinsa. Wannan kawai shi ne bambanci a tsakaninsu kukasance damu ako yaushe www.hausanet.ml