Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu A yau za mu yi
duba ne kan hanyoyin warware wata matsala mai cin tuwo a kwaryarmu mu mata . Matsalace da za mu iya kira da karama kuma babbar matsala. Karamar matsala ce in har
an san hanyar da za a maganceta, kuma babbar matsala ce in ba a san hanyar da za a bi wajen magancenta ba . Za mu tattauna ne a kan hanyoyin da zamu bi
don magance matsalolin bushewar gashin kai. Mata da dama na fama da wannan matsalar, wasu da zaran sun ji kan su ya bushe , maimakon su fara hada kwabin gashin kai
don magance wannan matsalar, sai kawai su dauko man gashi su shafe kansu da shi , wanda yin hakan na iya zama sanadiyar dankarewar gashi , toshe kofofin gashi da hana fitowarsa, musamman idan
gashi ya dade ba ’a wanke shi ba .
Sannan hakan zai iya bawa amosanin kai damar fitowa . Hanyoyin da za ki bi domin magance
bushewar gashin kai sune kamar haka Kwalliya ba ta cika sai da kai gyararre . Duk irin jan baki da hodar da za ki shafa , da jagira da zizaren da za ki saka ko ki goga, in har gashin kanki ba a gyare yake ba to, fa har yanzu da sauran kwalliya
Yan uwana mata, ina me yi muku sallama irin ta addinin musulunci 1. na farko Kwabin Ayaba
Kayan hadi
(Zuma cokali daya, Nunanniyar Ayaba ) Yadda ake hadawa 1 . Za ki bare bawon Ayaba sai ki markada a injin nika (blender ) ta markadu sosai
2 . Ki zuba zuma cokali daya ki gauraya su su hadu , sannan ki shafa a gashi tun daga karkashin sa har baki . 3 . Ki rufe kan da hular leda (shower cap). Bayan mintuna 15 - 20 sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi (Shampoo ) da na karawa gashi maiko (conditioner )
2 . Kwabin Kwanduwar kwai da Fiya
(Avocado ) Kayan hadi Kwanduwar kwai Fiya Yadda ake hadawa
1 . Za ki bare Fiya , sai ki zuba a injin
markade, ki zuba kwanduwar kwan ki a kai sai ki markada sannan ki shafa a gashin ki tun daga karkashin sa har baki. 2 . Ki samu hular leda ki rufe kan dashi . 3 . Bayan mintuna 15 20 , sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi da na karawa gashi
maiko (Shampoo and conditioner )
3 . Kwabin man Zaitun da man Kwakwa .
Kayan hadin
( Man zaitun Man kwakwa) Yadda ake hadawa
1 . Man zaitun za ki hada da Man kwakwa sai shafa hadin tun daga karkashin gashi 2 . Ki tufke gashin waje daya, sannan ki sa hular leda 3 . Bayan mintuna 15 - 30 sai ki wanke da sabulun wanke gashi da na karawa gashi maiko Ga masu laushin gashi yana da kyau
su yi amfani da na Ayaba , domin tana kunshe da sinadarin potassium wanda ya ke taimakawa gashin kai wajen sa shi ya yi karfi, yayi kyau .
Sannan yana da kyau don samun kyakkyawan sakamako, ki yi kamar sau biyu a sati Allah yasa mu dace daga naku www.hausanet.ml
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.