SHEIKH MUHD SALEH UTHAIMEEN yace azumi shine kamewa daga dukkan abinda zai karya azumi daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana da niyyar ibada,
Kuma an farlantata shekara 2 da HIJIRA
الالمام ببعض الاحكام تفسيرا واستنباطا
2HIKIMOMIN AZUMI‼
Kadan daga ciki=
1-barin abinda zuciya keso na ci & sha & jima'i da niyyar ibada
2-tunatarda mutum ni'imarda ALLAH yamasa na ci & sha & jima'i yayinda aka hanashi ita sai yasan muhimmancinta
3-mai wa data yadandana halin yunwarda talakawa ke fama dashi don yadubesu da idon tausayawa da taimakawa
4-wanke zuciya da taqawa da ladaftarda ita da hakuri & juriya
5-fa'idar lafiya da samun lada maiyawa
3 SIRRIN AZUMI‼
Kadan daga ciki=
1-yadda ake ladaftarda karamin yaro wajen hanashi wani abinda yakeso- haka ALLAH yake ladaftarda baligai manya abinda sukeso na ci & sha & jima'i
2-yana tarbiyyantarda bawa kwadayin abinda yake lahira- tahanyar barin abin kwadayinda yake duniya.3-yadda likita ke hana maras lafiya cin gishiri ko sukari don samun lafiyar duniya- hakama ALLAH yahana bawansa ci & sha & jima'i a yinin Ramadan don samun lafiya a duniya da lahira
4-ladfarda mutum yin afuwa da yafiya, ANNABI SAW yace "idan mutum yanada azumi sai wani yazageshi ko ya takaleshi- kada yarama- yace inada azumi
5-ladabtarwa akan IHLASI, mai azumi zai iya buya yaci ko yasha amma yakiyin haka don IHLASI
6-damane nabarin shaye shayen sigari & wiwi & muggan kwayoyi tunda ya hanu daga abu na wajibin rayuwa na ci & sha ai yafi sauki da yabar shaye shayen banza
7-yana tunatarda mutum wani hali na zaman kabari, domin cikin kabari ba ci ba sha ba kusantar iyali‼
4 FALALAR AZUMI‼
Kadan daga ciki=
1-samun gafarar ALLAH,
ALLAH SW ya irga wasu bayi maza 10 mata 10 cikinsu harda masu azumi- sai yayi musu alkawarin gafara da lada mai girma, [SRT AHZAB-135]
2-azumi yana kare azabar wuta,
ANNABI SAW yace "duk wanda yayi azumi don ALLAH- ALLAH zai nisantarda tsakaninsa da WUTA na shekaru 70" {MSLM-1164}
3-azumi sabulune wanda yake tsarkake laifin rantsuwa & zihari & kisan kai na kuskure & kurakuran mai Hajji da umara,
=cikin kaffarar rantsuwa akwai azumi 3
=kaffarar zihari= azumi wata 2
=idan mahajjaci ya yanka farce ko aski ko fesa turare cikin kaffarar akwai azumi
5 FALALAR RAMADAN‼
Daga ciki=
ANNABI SAW yace "idan RAMADAN yazo ana bubbude kofofin ALJANNA kuma akukkulle kofofin WUTA kuma adaure shedanu" {BHR-1898 & MSLM-1899}
2-Watane da ALLAH yasaukarda QUR'ANI acikinta, {SRT BQR-185}
3-samun DIMBIN garabasar albarkar LAILATUL QADR, {SRT QADR}
ALBARKAR SAHUR‼
ANNABI SAW yace "kuyi sahur lalle cikin sahur akwai albarka" {BHR-1926 & MSLM-1095}
ANNABI SAW yace "sahur albarkace kada kubarsa koda ku kurbi kurba na ruwa domin ALLAH da MANZONSA suna salati ga masu sahur" {AHMD}
ANNABI SAW yace kuyi sahur koda da loman tuwo {FAT'HUL BARY} IBN HAJAR yace= albarkar sahur anan yana nufin= samun kuzarin azumi/ saukake wahalhalun azumi/ farkawa alokaci mai falala da yin adu'a aciki/ bin sunna/ sabawa ahlul-kitab/ sababin yin sadaka ga mabukaci
GAGGAUTA BUDA BAKI‼
ANNABI SAW yace mutane bazasu gusheba da samun alhairiba muddin suna gaggauta buda baki {BHR-4957 & MSLM-1098} ABU HURAIRA ya kara da cewa domin yahudawa da nasara suna jinkirtawa
ANNABI SAW yace al'ummata bazasu gusheba akan sunnataba muddin baswa jinkirta buda baki zuwaga bayyanar taurariba tnz allah yasaka da alkairi amin
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.