Zuciyarki ta zama takarda, tawata zamabiro in rubata miki shafin kauna Kizama kofa na zamao makulli, mu hadu mubude kofar soyyar lambun
zuciyata Na kasa tsaye na kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban kaman wata a daren sha biyar Watau yau
da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar da haske zuciyata,domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk hasken raina Ki zama petur na zama inji mu hadu mu ta da lantarkin qauna ya shiba ta na baki filin zuciya ta ki shuka a duk wani lungun da sako bushiyar so a kauna don mu sami inuwar da zamu zauna muyi soyayya. Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwata ba ke lami ce ya rabin raina.Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na sha za ta haskaka zuciyata tayi fari. Rayuwata babu ke tamkar wayar da ba wayar chaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani. Kunne ya kurmance saboda
rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum. ya tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin
ganinki a yau da kullum Ya gangariyar madarar zumar da bata da gauraye, ya tauraruwa a cikin
jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta. Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya don ya gan ki.
Zuciyata na shan lawgadar zuma da madarar kauna Idon basira lafazin
rayuwata Alfijir na qauna ya keto,
tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a sararin Samantha tzu citata
Ya fankar da ke juya zuciyata, zan zamo kwale kwale ki shigo mu hau kan kogin so, in zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin kauna. Hadarin begen ki ya hado, guguwar sonki
ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi
na kaunar ki a filin zuciyata. Gaisuwa daga kamfanin so, harabar kauna,
gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwa ga rabin rayuwata. ya zare da allurar da ta dinken
zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutarlantarki ta zauna a nijeriya ya majaujawar zuciya ta, zan
zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin rijiyar soyayya.Ya tsokar zuciya ta, zan so ace ki zama fura in zama nono mu hadu a
kwaryar soyayya. Ya sahiba ta ki zama fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya. Ya masoyiyata, ki zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar da ke domin samun kalaman soyayya kawai ka kasan damu ako yaushe a wannan shafin www.hausanet.ml domin samun zafafan kalamai
Sunday, 13 May 2018
Subscribe Our Channel
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.