shugaba kungiyar wakan fina-finan Hausa na shiyya Arewa, guda cikin mawakan da suka fara waka a masana’antar shirya finafinan Hausa, shahararren mawakin da ya rere wakar Sangaya Sangandale da sauran wakokin da har yanzu taurauwar su ke haskawa a tsakanin masu sha’awar fina-finan Hausa. A tattaunawarsa da wakilinmu Sharfuddeen Baba a Kano, Musbahu Ahmad ya yi tsokaci kan halin da wakoki da mawaka suke ciki a yanzu, sannan kuma ya bayyana dalilansu na kafa Kungiyar mawakan irin ta farko Ga dai yadda tattaunawar ta kasance Bari mu fara jin wanda muke tare dashi? Alhamdulillahi ni sunana Musbahu M Ahmad Fadawa mai karatu takaitaccen tarihin rayuwar ka? An haifeni a unguwar Gwammaja dake Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, nayi karatun firamare da sakandire duk anan
Kano, sannan nayi Tahfiz Alqur’an a Jihar Bauchi, sai kuma karin ilimi da naje Kasar Maleshiya inda na karanta International House Ko ya Musbahu ya tsinci kansa a harkar
waka Ita harkar wakoki kasan komai yana da lokaci hakan Allah ya yi muka wayi gari muka ganmu mun tsinci kanmu acikinta tsundum, kasancewar ina da sha’awa a cikin
waka. Mun fara waka a kamfanin Sarauniya fims dake Gwammaja, dalilin zuwan da muke muna karbar fina-finai muna kallo, wannan ta bamu dama muka fara tattaunawa dashi daraktan kamfanin Aminu Mohd Sabo, Allah cikin ikonsa aka fara jarraba mu, muka samu
nasara na fara da fim din Allura da zare muka yi masu wakoki, har kuma zuwa lokacin dana yi masu wakar Sangaya wannan waka ta shahara kwarai a wannan lokacin ni ne nayi wannan waka. Kasancewar muryar Musbahu M. Ahmad sananniya ce a zukatan jama’a, shin ko za’a iya tunawa masu karatu wasu daga cikin wakokin da aka fara? Kafin Sangaya nayi wata waka a fim din
Allura da zare wadda mu biyu muka yi wannan waka ni da Mudassiru kasim shima sa’ana ne tare muka fara yin wakokin fina- finan Hausa, sai kuma wakar cikin Allura da Zare, sai wakar Na Gangaro, Samodara, Adali a fim din Tattabara, sai kuma Dawayya, Sangandali, Sanafahana da kuma irinsu Kakaki na Koshuwa duk wakoki ne irin na gargajiya duk ni ne na wallafa wadannan wakoki.
Da ka ambaci Sanafahana acikin wakar kamar a Nijar akayi wakar, shin gaskiya ne can din akayi wakar? Ni anan nayi wakar acikin studio amma wadanda suka sakata cikin fim sune suka yi tattaki har kasar Nijar kasancewar labarin ya
nuna haka, ni kuma dana tashi fitar da album din wakar munyi amfani da wata al’ada mun tafi kan ruwa, kamar yadda kowa yaga an sa
mata sunyi shigar Al’adar Hausa, yawancin abubuwan da kaga ni cikin faifan Bidiyo dole sai anje ire-iren wadanan wurare, amma ita wakar a studio aka yita. kasancewarka guda cikin wadanda suka fara rera waka a masana’antar shirya fina-finan kannywood ko ya zaka kwatanta wakoki ada da kuma yanzu?
A baya wakoki basu da yawa kamar yanzu haka kuma sakonnin ma suna tafiya dai dai da irin wancan zamanin haka na yanzu ma suke tafiya dai dai da irin wannan zamani,
duk da samun sauye sauye da akayi, ba sako kadai ake aikawa da wakar ba, akwai yanayin kida akwai yanayin murya da na’ura mai kwakwalwa ke gyarawa, duk wadanan abubuwa ana kallonsu, sannan kuma wakokin
sun banbanta, zaka ga abaya sakon kawai ake son isarwa, amma yanzu an fadada abubwa zuwa tallace tallace na haja, wakokin siyasa da Sarauta, saboda haka duk sai suka taru a cikin harkar waka. Wanann tasa ba irin sakonnin kadai ake ji ba. Da bamu da yawa mawakan a lokacin da wakokin ke da tasiri duka duka mu bakwai ne mawakan a wancan lokacinlWadanda suka fi shahara a wancan lokacin mu uku ne kadai, daga baya mutun biyu suka
karu aka kara samun wasu karin, duk zaka iya ji wakokin kowane mawaki a wancan lokacin, yanzu idan kace wakokin mawakan baki daya zakaji sai ka shafe mako biyu baka gama jiba. Wannan tasa yanzu ba zaka ji sakonnin kamar yadda aka saba jinsu a baya ba, zamani ya juyasu ana aro al’adu, wata wakar ma ta indiya ce za’a dauka da Karin da kidan a fassara, wata ta larbaci ce
sabanin mu ada sai munyi nutso cikin al’adun Bahaushe na gargajiya, lokacin dana ke fada maka cewa mawakan mu bakwai ne, to yanzu a
matsayina na shugaban mawakan shiyyar Arewa da muka tara mambobinmu tun lokacin da aka bamu rikon kwarya, a gabana
abinda muka samu mawaka da suka yi rijista da wannnan kungiya mutum 280 ne, kaga zai yi wuya ka kwakwanta da yadda tsarin yake a baya. Dole a samu canji tunani, ra’ayi, Al’adu, Ilimi da kuma wayewa ta zamani fiye da ta da. Kasancewar ka shugaban Kungiyar mawakan
shiyyar Arewacin Kasarnan, wane mataki ku ka dauka domin ganin an daidaita tafiyar ‘ya’yan wannan Kungiya domin kare kimarku?
Alhamdulillah daga cikin dalilan da yasa muka kafa wannan kungiya shi ne domin saita harkar wakar ta zama tana kan tsari, musamman rubutun ita Kanta wakar, sai
kuma ci gaban da za'a samu ta hanyar wakar. Sannan kuma ya za’a yi mawaki ya kasance mai kima da mutunci da daraja, kuma Alhamdulillahi mun samu hadin kan
mambobinmu, wanda ko a shekarar data gabata mun gudanar da taron karrama wasu mawaka tare da manyan Kasa, taron da aka gudanar a babban dakin taron fadar Gwamnatin Jihar Kano, wanda Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci wannan taro kuma shima an karrama
shi a wurin taron. Saboda haka yanzu muna da tsarin tace
wakoki bakowace waka zaka saki kawai ta shiga cikin al’umma ba, domin kaucewa batawa wani daga cikin Al’ummar mu. Alhamdulillahi anyi zaben shugabancin kungiyar a Jihar Kano inda aka bani rikon
kwaryar shugabancin kungiyar a matakin kasa, amma anan Kano ni aka zaba domin shugabantar shiyyar arewa, sai kuma Bili 0 shi ne sakatare, Muntari Kabara a matsayin
ma’aji. Muna cikin inuwar Kungiyar masu shirya fina-fina hausa ta MOPPAN. Kai ne shugaban Kungiyar mawakan Arewacin Kasarnan kuma anji wata badaqala data faru da sunan waka wadda Rahama
Sadau ta aikata, shin ko me zaka ce kan haka? Gaskiya wakarta bata ja mana komai ba a tsarin mu na mawakan Hausa, na farko adalcin da mutane da suka yi mana ba’a taba danganta wannan al’amarin da
mawakan Hausa ba, na farko ba wakar Hausa bace, sannan ba Musulmi ba ne kuma bama dan Arewa bane ya jagoranci wakar,
sanann ita akashin kanta Rahama Sadau ba mawakiya bace, jaruma ce a fina-finan Hausa. Amma wannan bai hana a tuntube mu ba Kungiyarmu na cikin inuwarMOPPAN
wadda duk taron da za’a yi dani ake yi, ina cikin mutum tara na farko da muka fara daga hannu don nuna amincewar mu da korarta daga masana’antar shirya fina-finai, damu aka rattaba hannu kan takardar
korarta. Kakarin da muke a wannan masana’anta shi ne me za muyi a kyauta Al’adunmu da Addininmu, duk abinda zai ci karo da Addininmu da Al’adunmu gaskiya zamu yi rigima dashi Muna sanar da jama’a cewar sana’a muke an sanmu da mutunci a garin nan¸ don haka ba zamu yarda wani bako ya tsallako ba da
wata Al’ada wanda shima idan kaje nasu garin ba Al’adarsa bace, saboda wata wayewa ya ja mana zagi ya barmu ana kallon mu mutanen banza, idan ka zagi
Musbahu a kalla sama da mutum dubu ne a garin nan zasu ji haushi, akwai Surikaina, Iyayena, Yayyena , Kannena, Surukan Kannena, saboda duk ina da alaka dasu. Amma idan bako ya tsallako ya yi zagi sai a
gama maganganun ma wani bai jiba.
Musamman kila shi Al’adarsa ta halatta masa haka. Wasu mutane sun shigo wannan masana’anta tayi masu sutura tana binsu bashin mutunta ta, amma kuma suna ja mata zagi, wadanda suka dabbaka sana’ar a nan Kano basu ja mata zagi ba balle ace masu ‘ya’yan kuka.
Gaskiya a layin da muka ja a halin yanzu ba zamu kyale kowane mutum ya zo yaci gaba da ja mana zagi ba balle mutumin da zai
tsallako, idan mutum ya ga ba zai iya kiyaye namu dokokin ba ya koma Jiharsu ko garinsu ya kafa tasa Masana’antar. Shin ko Musbahu na da shirin fitar da wani sabon album yanzu? Na kan dade ban fitar da album ba na kanyi shekara 4 - 5, album dina na karshe yau
shekararsa biyu, amma duk da haka ina kokarin sauyawa zuwa shekara daya ko biyu, na karshe shi ne Laila, kafin shi akwai Ban kwana da Masoyi, wadannan sune sabbin
album dina da suka fita wanda audio ne. banyi bidiyon suba, shima dan Almajiri ana bina bashi ban yi bidiyon sa ba har yanzu. Me yasa Musbahu Ahmad baya rawa a lokacin da yake gudanar da wakokinsa Ni da man haka na fara waka ta kuma haka
na san waka a wajena ni a nawa tunanin, a yanda na fahimci waka irin wakoki na basa bukatar rawa, bil’asali ma ni ban iya rawar
ba, ko da ma zanyi ba dole tayi min kyau ba tunda ka ga ban iya ba bai kamata ma na fara ba. Ni ban dauki rawa da cewar sai ka alakanta
ta da waka ba. Wakoki na sako ne wata Magana suke aikawa, idan ana saurarar waka ta idan na kama rawa, shin rawar za’a kalla ko sakon dana ke fatan isarwa zai saurara
Bukata ta a saurari wakar ka fahimci sakon da ke cikinta, sakon dana ke aikawa ya isa wurin da na ke fata ko kuwa bai isa ba wannan shi ne babban buri na a waka
Shin ko wa Musbahu ya fi gamsuwa da yin waka tare da ita cikin masu amsa masa wakokinsa? Kwarai ina da mutanen dana saba wakoki
dasu, wanda aka fi jin wakoki na dasu, amma ba wai suna ajeye kawai don yimin amshi ba, suma zaman kansu suke suna aikinsu, amma ni idan na fara rubuta waka ina hangen muryar wacece zata dace da wannan waka, idan ana daga murya sosai nasan wadda zan
kirawo ta hau wannnan sautin, haka idan kasa kasa nake yinta mai sanyi akwai wadda na tabbata zata fi dacewa da wannan amshin. Shi yasa aka fi jina da mace daya wajen yin
wakoki na.bKo mene sakonka na karshe ga ‘yan uwa mawaka da sauran Al’umma?
Alhamdulillah sakona na farko ga mawaka ne aji tsoron Allah a duk inda suke, duk abinda za kayi ka tuna Ubangiji ka sani Duniya zuwanta kayi kuma barin ta zaka yi, Kafin kai wani yazo ya tafi, idan takamarka ka shahara wasu sun shahara kafin kai, kuma yadda suka sauka haka kai ma wata rana dole ka sauka. Wakar zagi ni ban yarda da ita ba, ka ci mutuncin wani cikin waka don wani abin Duniya hakan ko kadan bai dace ba, dole mutum ya kiyaye harshensa kwarai da gaske, a kiyayi zarmewa da banbadanci cikin wakoki, ka zama wani maroki ko wani abu daban. Al’ummar gari kuma su ci gaba da bamu hadin kai tare da yi mana Addu’a, sannan su taya mu duk abinda su ka ga na gyara muna yi don gyaran wannan masana’antar ce, idan muka tsaya akan gaskiya ya kamata suma su tsaya akanta, abin mamaki sai wani abu ya faru damu sai ayi caa ana zaginmu, idan kuma ya faru muka dau mataki akashin kanmu sai kuma su dai mutanen kaji suna cewa ba’ayi adalci ba, wanda da an kyaleshi, sune zasu ci ga da tsine mana albarka. Haka ta faru lokacin fim village aka dinga dauko hotunan su Ali Nuhu da suka yi fim wanda ba na Hausa bane, amma sai aka dinga yanko hotunan su hade da mata ana nuna mana ana zagimu ana tsine mana, yanzu wani abu ya faru da ‘yarmu Rahama Sadau mun hukunta ta kafin ma Duniya tasani munce bamu yarda da wannan ba, munja layi da wadannan abubuwa, sai kuma ka ga wasu daidaiku sun shiga social media suna kaimana harehare iri daban daban cewa bamu hukunta wane da wane ba, kaga wannan ba adalci bane, idan munyi shiru ku
zage mu, idan munyi hukunci kuma a
zagemu, saboda haka muna rokon mutane suyi mana adalci, su kyale mu sana’ar mu ce mu yiwa kanmu da kanmu hukunci don gyara sana’armu Dan Allah mukula sosai daga www.hausanet.ml
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.