. SAYE DA SAYARWAN YAN WASAN KWALLON KAFA TA DUNIYA - hausanet hausanet





Saturday, 12 May 2018

Home SAYE DA SAYARWAN YAN WASAN KWALLON KAFA TA DUNIYA

Subscribe Our Channel


Chelsea ta bayyana cewar babu wata kofa ga dan wasanta Eden Hazard, na barin kungiyar don komawa kungiyar
Manchester united a yanzu. Chelsea ta fadi hakanne bayan da wasu magoya bayan kungiyar suke rokon sa da ya koma wasa a karkashin tsohon Kocinsa Jose Mourinho wanda yanzu yake kungiyar Manchester united. Har ila yau dan wasan gaba na Chelsea, Alvaro Morata, mai shekaru 25, na shirin
barin kungiyar dan komawa kulob din Juventus, inda ake ganin Chelsea zata mai da hankalinta wajan ganin ta dauko dan wasan PSG Edinson Cavani, dan shekaru 31 da haihuwa.
Arsenal tana yunkurin ganin ta dauko Kocin Juventus, Allegri ko kuma tsohon Kocin Barcelona Luis Enrique, don kasance mata koci a shekara mai zuwa sai dai a gefe guda duk kansu suna duba yuwar zuwansu domin yanayin tsare
tsare na hukumar gudanarwa ta

Kungiyar ta Arsenal. Haka kuma Kungiyar ta Arsenal ta ce tana da karfin gwiwar cewar dan wasanta
Jack Wilshere, zai sabunta kwantirakin sa don cigaba da zama a kungiyar Kungiyar Bayern Munich ta ce a shiye take da ta sayar da dan wasan gabanta dan kasar Poland Robert Lewandowski, wanda Manchester united da Real madrid
ke da burin ganin sun dauko shi a
karshen kakar wasan bana.
Shugaban kungiyar kwallon Kafa ta
Barcelona ya ce kulob din ya fara
tattaunawa da dan wasanta Samuel
Umtiti, kan sabunta kwantirakinsa a
kungiyar kasancewar Manchester united, ta nuna sha'awarta kan dan wasan mai shekarun haihuwa 24 a duniya aha dakyau domin Karin labaran musayar yan wasa kawai kubimu a wannan shafi www.hausane.ml