. MAGANIN SANKO - hausanet hausanet





Friday, 11 May 2018

Home MAGANIN SANKO

Subscribe Our Channel


Masana kimiya da fasaha  sun gano cewa maganin yana tasiri a ramin gashi a gwajin da suka yi inda yake sa gashi ya tsiro Yana kunshe da wani sinadari da ke dakile tasirin
sindarin Protein da ke sa gashi ya zube da haifar da sanko. Jagoran ma su binciken Dakta Nathan Hawkshaw ya shaidawa cewa za a yi gwaji domin a tabbatar da maganin ba shi da illa ga mutane. A yanzu magunguna biyu ne kawai ake da su nama su sanko Maganin minoxidil, na mata da maza. maganin finasteride, na maza kawai Sai dai dukkaninsu na yin illa a jikin bil'adama, shi ya sa a mafi yawan lokuta masu sanko ke zuwa asibiti domin yi mu su dashen gashi. Binciken da aka wallafa a Mujjalar PLOS Biology an yi shi ne a cikin wani dakin gwaji inda aka yi amfani da samfuri da ke dauke da gashin wasu maza su fiye da arba'in wadanda aka yi wa dashen gashi Masu binciken daga jami'ar Manchester, sun fara aiki ne kan wani sindari da ake kira cyclosporine
A, wanda aka yi da shi tun daga shekarun 1980 a kan marasa lafiya da aka yi wa dashen koda ko hanta da saraunsu

--->Masana kimiyar sun gano cewa maganin na rage tasirin sinadarin protein da ake kira SFRP1 wanda yake da muhimmanci wajan ragewa da kara tsawon gashi. Sai dai saboda illar CsA ba za a iya amfani da shi ba akan ma su sanko Masu binciken sun sake yin nazari kan wani sinadari da ake kira WAY-316606 kuma sun gno
cewa yana tasiri sosai wajan rage kaifin sinadarin protein Dakta Hawkshaw ya ce maganin zai iya sauya rayuwar mutane ma su sanko
To Allah ya taimaka