Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya ce abu ne mai matukar wuya a iya has ashen waye zai yi nasara a zaben shugaban kasa da za a yi tsakanin manyan ‘yan takara; shugaba Buhari na jam’iyyar APC mai mulki da Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP.
A cewar Ekweremadu, sanin wanda zai lashe zaben shugaban kasa tsakanin Atiku da Buhari zai yi wuya ne saboda yadda ‘yan takarar biyu ke da karfi da magoya baya. Ekweremadu ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi daga ma su sauraron hirar da aka yi da shi a gidan Radiyon Urban FM 94.5 a jihar Enugu, a jiya, Asabar. Da aka tambaye shi don yin has ashen wanda zai nasara tsakanin Atiku da Buhari a zaben da za ayi ranar 16 ga.wata, Ekweremadu ya ce bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a siyasance, zai yi wuya a iya hasashen wanda zai yi nasara a tsakanin ‘yan takarar biyu.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.