. MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin DADIN KOWA - hausanet hausanet





Wednesday, 6 February 2019

Home › › MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin DADIN KOWA

Subscribe Our Channel



MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI

JAN KUNNE GA TASHAR

AREWA24 Cikin Shirin (DADIN KOWA)

Muna kallon shirin dadin kowa Muna kallon yadda kuka shirin Yaki da Malaman AL-QURANI Domin tozarta ALMAJIRCI Ta hanyar dora malam NA TA'ALA (MATO YAKUBU) da bashi

damar tozarta AL QUR'ANI kai tsaye domin wata manufa ta yahudu akan Almajirci da nunawa wadanda ba musulmai ba su fahimci dukkan malamin AL QUR'ANI a matsayin mutum me son zuciya da son kai wadda bai isa akan komai ba.

JAN KUNNE

A matsayin mu makusanta makaranta AL- QUR'ANI muna kira da babbar murya cewa ya zama dole a gyara ko kuma muma mu daura Dammarar yaki daku a makarantun mu na zaure da tsangayu da islamiyyu ta hanyar aika muku da ADDUO'I na musamman har sai ALLAH YAYI

MANA MAGANINKU. JAN KUNNE GARE KA WATO YAKUBU (NA

TA'ALA) (Allah Ya Shirya).

Ya zama dole ka gyara irin siffofin da kake siffanta makaranta AL QUR'ANI domin cimma manufarka ta tozarta malaman AL QUR'ANI da

wulakantasu ka sani cewa ka shirya fito na fito Ne da LITTAFIN ALLAH dukkan wadda ya shirya haka babu shakka ya durfafi hanyar fito na fito ne da 

MAHALICCIN WANNAN LITTAFI ALLAH (SWT). KIRA GA MUTANE MUSAMMAN MA

MAKARANTA AL- QUR'ANI Mutaimaka Wajen Yada Wannan Saqo Har Ya Isa Ga Masu Shirya Wannan Shiri Wato Hukumar Gidan Area24.

Muhammad Ahidan Bako ArifullahAllah Ya Kwauta. Ameeen