. Ban Umarci Duk Wani Mabiyina Ya Yi Zabe Ba Sakon ----Shaik Zakzaky - hausanet hausanet





Tuesday, 5 February 2019

Home › › Ban Umarci Duk Wani Mabiyina Ya Yi Zabe Ba Sakon ----Shaik Zakzaky

Subscribe Our Channel




Ban Umarci Duk Wani Mabiyina Ya Yi Zabe Ba, Sakon Shaik Zakzaky Daga Inda Ake Tsare Da Shi Maganganu sun yi ta yawo kan yiyuwar shigan yan Shi'a babban zabe me zuwa a kasar nan da za'a fara ranar 16 ga watan biyu. Wanda a bayaN yan shi'an sun kasance suna kauracewa yin harkar zaben a shekarun baya su zaba ko su shiga a zabesu. Amma cikin kwanakin nan maganganu sun tsananta kan mabiya shi'a wandanda gwamnati me mulki ke tsare da jagoransu shekaru 3, kan yiyuwar su shiga ayi dasu Wasu rohatanni sun bayyana cewa mabiya shi'an da suke da yawa a wasu daga jahohin arewacin kasar nan wanda ana fadin adadinsu yakai miliyoyi zasu bada dukkan kuri'unsu ga Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin Jam'iyar Adawa ta PDP. Daga bangaren jami'an tsaro kuwa suna Raba takarda ga hukumomi cewa mabiya shi'an Suna shiri tada hargitsi a lokacin zaben, inda tuni mabiyan shi'an suka karyata hakan tare da jan kunne A ranar Asabar 26/01/2019, wasu daga makusantan Shaik Ibraheem Zakzaky sun ziyarce shi a wajan da ake tsare da shi sannan ya yi magana kan zantukan da ake yadawa kansu akan zaben yana cewa “To mu muna Zabe ne? Ina ruwan mu da zaben su. Kuma ma mu ai ba'a sanmu da hargitsi ba, idan ma haka ne. Su kansu wannan al'ummar sun yi mana Shaida akan cewa mu ba masu hargisti bane” inji shi Rariya.com

  1. We are not politician,so how can we vote and been voted?

    ReplyDelete
  2. Dashi da bashi,daku da Baku zamuyi zabe inshaa Allah Kuma Wanda bakaso shizaici

    ReplyDelete