. INEC ta kara wa'adin raba katin zabe - hausanet hausanet





Friday, 8 February 2019

Home › › INEC ta kara wa'adin raba katin zabe

Subscribe Our Channel



Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da kara wa'adin rarraba.katinan zaben daga yau juma'a zuwa litinin 11 ga watan Fabrairu. Karin na kwana uku ya kunshi har da ranakun Asabar da Lahadi. INEC ta ce ta Kara wa'adin ne bayan kiranye-kiranyen da ta

samu na neman a kara wa'adin raba katinan zaben. A baya dai hukumar ta ce akwai miliyoyin katunan zaben da masu su ba su je sun karba ba.Akwai daruruwan 'yan Najeriya da ba su karbi katinsu na zabe ba, kuma hukumar zaben kasar ta ce duk wanda bai karbi katin ba zai yi zabe ba. Hukumar zaben kasar kuma ta ce bayan wa'adin da ta diba ya kawo karshe a ranar Litinin 11 ga Fabrairu, za ta mika ajiyar katinan zaben da ba karba zuwa Babban Bankin Najeriya har sai an kammala zabe inda za a ci gaba da rijista da kuma raba katinan.