PAGE 1
Tana Zaune a dakinta ita kadai tanata
faman rubuci rubuce Dare ne sosai kusan biyu saura gari yayi tsit bakajin
komi sai rugugin hadari dayake
haduwa Zeenatu kenan jajirtacciyar "yar
jarida wacce takasance batada tsoro a ckn ranta arayuwarta bataki tayi qunar bakin wake ba inhar zata cimma burinta
Inta d 'anyi rubutu jim kadan saita
dakata tayi tsai da ranta ta kalli silin din dakinta kana taci gaba Ahanakali aka turo dakin aka shigo Ta dago kai da sauri takalli me shigowar Mahaifiyar tace gwagwgo Sa,a Yanxu ashe bakiyi bacci ba zeenatu har yanzun kinata faman wannan rubutce rubucen naki na wahala ayi mutum baxai hutawa ransa ba nifa
gaskiya nafara tsanar aikin nan maku zinatu domin bakya hutawa ko kadan kuma bakya kallon hatsarin dake ciki ina dalilin hakan. Zeenatu tayi murmushi tace da gwagwgon kwantar da han kalinki gwagwgo na yanzu xan ajiye
nakwanta dan allah kidaina damun kanki da Tsaurin da aikina kedashi Duk wani abu na hatsarin ciki da yardar Allah bazai kusanceni ba kiyita min addu,arki nasan Allah zai tsareni To hakane Allah yatsareki da tsarewarsa Amma nikam
yanda nakejin wasu "yan jaridun ke
shiga taskun rayuwa inajiye mk tsoro yar nan da zaki ajiye wannan aikin ki sami wani da zanfi farin ciki. Zeenatu tace
" oh kash gwaggo kenan yaushe zanyi
kasadar ajiye aikin dana samu awahalce haba ai yanda ma nake kaunar aikin jarida banga abinda zaisa na karaya kona fasa yinsaba ai duk tsanani yana
tareda sauki kin manta wahalhalun dana sha kafin nasameshi ? Kin manta irin gwagwarmayar rayuwar da nayi gwaggo
akan karatun aikin jarida ke kanki kinsha tausayan akan fafutukar dana ringayi wajen buga bugar ganin nakammala karatuna kema ai yau innace nadaina aikin jaridar nan saikiyi min fada ko kin
manta tun ina karamata nake sha,awar naga nakasance
YAR JARIDA ne?
Gwagwgo taja ajiyar gwauran numfashi tace "to ya zanyi dake yar nan amma gaskiya ina ckn jin tsoron yanda kike kai dare kafin kishigo gida tunda kince wani
xubin bakya samun abin hawan dazai
shigo dakelungun nan namu gashi antaba biyoki kwanaki abaya kartai Allah yasa kika farga dasu Allah kuma yatsareki kk tsallake rijiya da baya Zeenatu tace " hhhhmmm wannan
abun ai ya zama shudadde kima daina tunashi ya wuce guna sau fatan Allah yatsare ni agaba. to Amin Amin dai, yanzu dai yakamata ki kwanta
haka Zeenatu ta ajiye biron dake hannunta tace " to gwagwgo na yanzu ma kuwa zankwanta da sassafe naci gaba don da wuri zan futa ma. Gwagwgon na futa ta kwanta akan
katifarta Zamuci ga kudan dakacemu
Daga www.hausanet.ml
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.