. - hausanet hausanet





Tuesday, 23 October 2018


Subscribe Our Channel


Zakuji Cewa : Real Madrid Tana Dab Da Korar Kocint Sannan : Akwai Matsala A Real Madrid, cewar
Zidane Abin mamaki : Mourinho Zai Koma Real Madrid Bazamu soba : Marcelo Yana Son Komawa Jubentus Duka a cikin labaranmu nayau 23 Oct 2018 Real Madrid Tana Dab Da Korar Kocinta Rahotanni daga kasar Sipaniya sun tabbatar da
cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana dab da korar kociyanta, Julian Lopetegui, bayan ya samu nasara a wasanni biyar kacal cikin
wasanni 12 da kungiyar ta buga a karkashinsa. Lopetegui, wanda yakarbi aiki a hannun tsohon
kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, yabar aikin koyar da kasar Sipaniya ne bayan da shugabannin kwallon kafa ta kasar suka koreshi
bayan ya cimma yarjejeniyar zama kociyan Real Madrid ana dab da fara gasar cin kofin duniya. Lopetegui yafara buga wasa a kungiyar da kafar hagu bayan da yayi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid a wasan
karshe na cin kofin Super Cup na nahiyar turai daci 4-2 a farkon watan Agusta. Har ila yau Real Madrid tasha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow ta kasar Rasha a gasar cin kofin zakarun turai da aka buga kafin a tafi hutu a satin daya gabata kafin
kuma su sake yin rashin nasara a hannun Lebente a wannan satin har gida. Real Madrid dai a halin yanzu tayi wasanni biyar batare data samu nasara ba kuma hakan yasa
aka fara rade radin cewa kungiyar zata sallami kociyan domin kada wankin hula yakaisu dare.

Real Madrid dai zata buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Bictoria Plazen kafin kuma ranar Lahadi su buga wasan hamayya da kungiyar
kwallon kafa ta Barcelona
Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa kungiyar a yanzu tana cikin wani hali daya kamata mahukuntan kungiyar su tashi tsaye kafin abubuwa suyi yawa.
Real Madrid mai rike da kofin gasar zakarun turai, ta sake shan kaye a karo na hudu cikin wasanni biyar da ta fafata a jere, bayanda Lebante ta je har gida ta samu nasara kanta da
kwallaye 2-1 a gasar La Liga.
Rashin nasarar dai ta sanya kungiyar ta Real Madrid kafa tarihin fuskantar koma baya mafi
muni a kakar wasa da taba gani, tun bayan shekarar alif 1985 da kungiyar ta taba fuskantar irin wannan matsalar. Wannan kalubale yasa a halin yanzu, mai horar da kungiyar Julen Lopetegui kara fuskantar
matsin lamba fiye da kowane lokaci, ganin cewa a mako mai zuwa Real Madrid za ta fafata wasan El Clasico da babbar abokiyar hamayyarta
Barcelona. A halin yanzu dai Real Madrid ke a matsayin ta 7 a gasar La Liga da maki 14, yayinda abokiyar
hamayyarta Barcelona ke jagorantar gasar da maki 18, bayan lallasa Sebilla da kwallaye 4-2.

A baya bayan nan dai, wasu kafafen yada labaran Sipaniya, sun rawaito cewa, akwai yiwuwar Real
Madrid ta maye gurbin kocinta Lopetegui da tsohon mai horar da Chelsea Antonio Conte,
Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana duba yiwuwar sake daukar tsohon kociyan kungiyar
Jose Mourinho domin yakoma kungiyara karo na
biyu. Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana cikin wani hali a hannun mai koyarwa Julian
Lopetegui wanda yazama kociyan kungiyar a wannan kakar bayan Zidane yabar aikin horar da
kungiyar. Kungiyar dai ta buga wasanni biyar bata samu nasara ba kuma acikin wasannin kwallo daya kawai ta zura a raga a wasan da suka sha kashi a hannun kungiyar Lebente daci 2-1 har gida a gasar laliga. An ruwaito cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana bukatar canji a kungiyar kafin wasan
da zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta

Barcelona a karshen sati yayinda kuma aka bayyana cewa kungiyar zata bari taga abinda zai faru a wasan da zata buga da Barcelona. Sai dai mutane da dama zasuyi mamaki idan har ta tabbata Mourinho, wanda yake aiki da Manchester United a yanzu ya koma Barcelona idan aka duba yadda akayi yabar kungiyar a shekarun baya. Shima dai Mourinho yana cikin halin rashin tabbas a kungiyar Manchester United bayan da kungiyar bata fara buga wasannin wannan kakar cikin nasara ba sai dai Real Madrid har yanzu tana ganin Mourinho wani shahararren kocine bayan ya lashe kofin laliga da Copa Del Rey a lokacin daya zauna a kungiyar daga shekara ta 2010 zuwa 2013 Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Marcelo, dan kasar Brazil, ya bayyanawa kungiyarsa ta Real Madrid cewa yana son barin kungiyar domin komawa Jubentus da buga wasa.
Marcelo, wanda a kwanakin baya aka dangantashi da komawa Jubentus sakamakon komawar dan wasa Cristiano Ronaldo kungiyar ya
taba bayyana cewa yanajin dadin zaman Real Madrid sai dai kawo yanzu maganar tashin dan wasan ta dawo.

Marcelo wanda yakeson barin kungiyar sakamakon rashin kokarin kungiyar ya bayyana cewa yana son barin kungiyar zuwa Jubentus
idan abubuwa basu gyaru ba a kungiyar nan da watan Janairu.
An ruwaito cewa shugaban kungiyar, Florentino Perez, bayajin dadin bukatar da Marcelo ta barin
kungiyar sai dai idan dan wasan ya takura zai tafi kungiyar zata iya bukatar fam miliyan 44 ga duk kungiyar da take son daukarsa.
Sai dai Jubentus itama zata amince da biyan abinda Real Madrid zata bukata akan dan wasan ta hanyar siyar da dan wasanta na baya Aled
Sandro wanda kungiyoyin firimiya suke bukatarsa. Marcelo dai yakoma Real Madrid a shekara ta 2007 kuma tun bayan zuwansa ya buga wasanni
460 a kungiyar a dukkannin wasannin data buga daga shekarar sannan ya lashe kofuna da dama a kungiyar. Wani hasashe zakayi dan gane da ficiwar marcelo a Madrid?