Ban san yaya aka yi rayuwata ta
susuce ba – Zainab Indomie
Fitacciyar jarumar da aka daina yayinta, Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yaya aka yi rayuwar
aktin dinta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a.masana’antar fina-finan Hausa.
Jarumar ta ce ta samu daukaka tun tana karama,
amma saboda kaddara ba ta san abin da ya faru ba yanzu ta rasa komai. Ta ce, “Na samu daukaka tuna ina karama, wani abu ya faru yanzu dai na rasa komai, babu
ganganci a ciki, ba na kuma ganin laifin kowa, ban kuma zargi kowa ba sakamakon mawuyacin
halin da na shiga. “A halin da ake ciki ba zan iya tunawa da komai
ba, ba zan iya cewa ga abin da ya sa na samu kaina a cikin mawuyacin hali ba. Idan har laifina.ne ina rokon Allah Ya yafe mini, idan ma laifin
wani ne to Allah Ya yafe masa,” inji ta. Jarumar ta kuma roki Allah Ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya..Ta ce, “Na gode wa Allah saboda jarrabawar da
ya yi mini, ina rokon Allah Ya fitar da ni daga wannan jarrabawar. Na mika kaina ga hannun Ubangiji
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.