LABARAN WASANNIN
KWALLON KAFA NA DUNIYA
INTER MILAN TAFARA NUNA SHA'AWARTA AKAN MALCOM
Barcelona ta dauko Malcom aliviera daga Bordeaux akan kudi €41M
Dan wasan yashafe wata uku a Kungiyar ta Barcelona ahalin yanzu
Malcom yagaza samun dama a Kungiyar karkashin jagorancin enestor valverde
Inter Milan tashirya fara tattaunawa da Kungiyar ta Barcelona akan yuwar sallamar mata dashi a watan January
REAL MADRID TASHIRYA BADA GARETH BALE DOMIN DAUKAR HARZARD
Tun bayan da mai horar da Kungiyar ta real Julian lopetegui yabayyana cewa shi yafi son Hazard akan Neymar Jr
Ahalin yanzu dai real Madrid tashirya bawa Chelsea Gareth Bale tareda cikon kodaden amma ba abayyana adadin kudinba
Real Madrid tashirya tsaf domin siyan danwasan a watan January
RONALDO YASHAWARCI JUVENTUS AKAN SU DAUKO RAKITIC
Kungiyar kwallon kafata juventus bayan tanuna sha awarta nadon daukar dan wasan Barcelona jordi Alba
Jordi Alba Wanda bayjima dakarawa Barcelona contract ba
Alba Wanda yatsawaita zamansa a Kungiyar harzuwa 2020
Bayan Kungiyar ta
Bayan jordi Alba anasa bangane Ronaldo yabukace akawo dan wasan kasar Croatia Ivan rakitic
WENGER YABAYYANA RASHIN WAKILTAR GERMANY DA OZIL YADENA HAKAN KA'IYA SHAFAR KARSASHIN DAN WASAN
Ozil dai yabayyana ajewa Germany Riga bayan angama cin kofin duniya (world cup) Russia 2018
Tsohon mai horas da Kungiyar kwallon kafata Arsenal Arsene Wenger yabayyana cewa rashin bugawa kasarsa ta Germany da Ozil yadeina tofa hakan zaiyi matukar tasiri wajen ragewa dan wasan karsashi a tsakiyar fili
Anasa bangaren mai horas ta yan wasan kasar Germany Joachim low ya bayyana bukarsa nason dawo da ozil din cikin tawagar yan wasan kasar Germany
RAHOTANNIN KUNGIYOYIN KWALLON KAFA DABAN DABAN
Kungiyar kwallon kafata west ham utd tashirya tsaf wajen daukar dan wasan Chelsea Olivier Giroud maishekaru 32
Dan wasan kasar France da Manchester united Paul pogba mai shekaru 25 yabayyana burinsa nason zuwa Barcelona a season mezuwa
Jaridar (mail) ce tabuga wannan labarin
Dan wasan tsakiyar Manchester united Andreas Pereira yabayyana cewa tafiyar pogba daga Manchester united zuwa wata Kungiyar tofa hakan zaizamo Abu Wanda babu tinani kwatata acikinsa indai akayarda akabarshi yabar Kungiyar
Pereira yabayya hakanne awani video daya dora ashafinsa na Instagram
Liverpool da Manchester united na rububin matashin dan wasan PSV mai shekara 21 mai suna Steven Bergwijn
Arsenal ce kangaba wajen zawarcin dan wasan tsakiyar Cagliari Nicolo Barella maishekara 21 aduniya
Juventus da Manchester united sunbi sahun Barcelona wajen zawarcin danwasan bayan Kungiyar kwallon kafata Ajax Matthijs De Ligt
An bayyana farashin dan wasan zaikai €50M daidai da £43M (Goal.com)
Dillalin dan wasan bayan juventus Daniele Rugani yamusanta raderadin da ake nacewa dan wasa Rugani zai tsallaka Chelsea daga Juventus
Manchester city da Manchester united dukkansu sunmaida hankalin su wajen zawarcin danwasan bayan inter Milan maisuna Milan skriniar mai shekaru 23 anasaran danwasan zai tsallaka gasar EPL amma ba abayyans Kungiyar dazai komaba
NEYMAR YABAYYANA SHA'AWARSA NASON BARIN PSG A SEASON MEZUWA
Jaridu dadama sun maids hankalin su wajen kawo wannan labarin musammanma jaridar metro.us dakuma (mundo deportivo)
Dan wasan yabayyana sha awarsa na barin PSG zuwa tsohuwar Kungiyar sa ta Barcelona wadda yabari
Neymar Jr mai shekaru 26 nahaihuwa aduniya yabbayana cewa baya jin dadin Kungiyar ta PSG a ahalin yanzu
Jaridar Mirror(sky sports News) tabayyana cewa Kungiyar kwallon kafata Barcelona tashirya biyan kudin da shugaban Kungiyar ta PSG Nasser Al-khelaifi zai bukata akan danwasan kasar Brazil din Neymar Jr
Dan wasan Wanda yashafe season daya a kungiyar yakuma jefa kwallaye 25 cikin wasanni 27 daya wakilci PSG
Neymar yasamu nasarori dadama a Kungiyar ta PSG irinsu
Nasarar lashe kofuna dadama.
Ligue 1
Coupe de France
Coupe de la ligue
DA sauransu
JERIN YAN WASAN GASAR EPL WADANDA BASUDA CIKAKKIYAR LAFIYA
Bayan yanwasa sundawo daga wakiltar kasashensu, wasu daga cikin yanwasa sunsamu rauni irinsu
Robert Snodgrass na west ham utd
Danny Rose na Tottenham
Victor wanyama na Tottenham
Alex McCarthy na Southampton
Ciaran Clark na Newcastle
Nemanja Matic na Manchester united
Maroune Fellaini na Manchester united
Scott McTominay na Manchester united
Virgil van Dijk na Liverpool
Sadio mane na Liverpool
Mohamed Salah na Liverpool
Navy keita na Liverpool
Idrissa Gueye na Everton
Wilfried zaha na Crystal palace Ethan Ampadu na Chelsea
Stephen Ward na Burnley
Danny Welbeck na Arsenal
Sokratic na Arsenal
Inda akesaran wasu zasu iya wakiltar Kungiyoyin su awannan satin wasu kuma sai sunyi jinya
LUKE SHOW YA KARA KWANTARAGINSA A MANCHESTER UTD
Dan wasan maishekaru 23 aduniya Wanda Manchester united ta dauko daga Southampton ya tsawaita zamansa a Kungiyar ta Manchester united Inda yakara kwantaragin shekara 5
DAN WASAN TOTTENHAM ERICKSEN YADAWO DAGA INJURIN DAYA TAFI
Fitaccen danwasan kasar Denmark da Kungiyar kwallon kafata Tottenham cristian ericksen Wanda yashafe makonni Yana jinya, yanzudai dan wasan tsakiyar ya murmure kuma anasaran danwasan zai buga wasan da Kungiyar sa ta Tottenham zata karda west ham utd agobe asabar
BARCELONA TAFARA NEMAN DAN WASAN BAYAN RB LEIPZIG
Kungiyar kwallon kafata Barcelona tafara zawarcin matashin danwasan baya maishekaru 19 nahaihuwa aduniya
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.