. GOODLUCK YA BAYYANA DAN TAKARARSA NA SHUGABAN KASA A ZABEN 2019 - hausanet hausanet





Saturday, 13 October 2018

Home GOODLUCK YA BAYYANA DAN TAKARARSA NA SHUGABAN KASA A ZABEN 2019

Subscribe Our Channel



A ranar Asabar din da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana mafificin zabinsa cikin manema tajarar kujerar shugaban kasar nan da za su fafata a yayin babban zabe na 2019.



 Jonathan yayin
bayyana zabinsa cikin manema takarar kujerar shugaban kasar ya bayyana cewa, ba bu wani dan takara da zai iya hada kan al'ummar kasar
nan wuri da face tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark. Tsohon shugaban kasar yake cewa, David Mark shine kadai yake da
cancanta gami da nagarta ta hangen nesan da zai iya fayyace tsakanin daidai da rashinsa wajen hada kan al'ummar kasar nan a 2019.


 Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, Jonathan ya bayyana hakan ne yayin da tsohon shugaban majalisar ya ziyarce shi har gidansa dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa. Ya ci gaba
da cewa, ba ya ga kalubale na gurbacewar tattalin arziki da kalubale na tsaro, shugaban kasar Najeriya na gaba zai kuma fuskanci babban kalubale na rashin hadin kan al'ummar kasar nan. Majiyarmu ta fahimci cewa, Jonathan


yana kyautata zaton samun nasarar jam'iyyar PDP a babban zaben na 2019, ya kuma bayyana cewa ba bu mafificin dan takara da ya kamata al'ummar Najeriya su dankawa amanarsu a hannu face David Mark