. Hadiza Gabon Ta Soma Fitowa A Finafinan Turanci - hausanet hausanet





Thursday, 17 May 2018

Home Hadiza Gabon Ta Soma Fitowa A Finafinan Turanci

Subscribe Our Channel



Fitacciyar jarumar nan ta finafinan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a finafinan Nollywood da ake yi a kudancin Nijeriya. Jarumar ta shaida wa BBC Hausa cewa ta fara
gwada sa'arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin finafinai a
bangarori daban-daban. A cewarta, "Ba wannan ne karon farko da na
soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina- finan Nollywood. Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa

mai sunavLagos real fake life Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a
matsayin 'yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a
wannan fim Hadiza Gabon ta kara da cewa "Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida
masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba
Jarumar ta ce babu wani "bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don
haka na ji dadin soma fitowa a
Fina nan