Matsalar rashin kudi da kuma tsadar Rayuwa ta soma tilastawa wasu magidanta guduwa suna barin iyalansu, batun da yanzu ke kara barazana ga rayuwar ma’aurata.-- A baya bayan nan wani magidanci mai suna Mallam Muhammad, ya arce biyo bayan haifa masa yan uku da mai dakinsa ta yi, da yanzu haka take kwance a babban asibitin kwararru da yaran da ta haifa cikin mawuyacin hali. Yan uku Malama Maryam itace matar data haihu, ta kuma bayyanawa majiyar mu halin da suke ciki a yanzu ita da jarirai Ukun data haifa. tace “Na gode Allah, wannan shine haihuwata na Uku, domin ina da yara Hudu, kuma tun Lokacin da nazo awo bayan da likitoci suka duba ni, suka yi hasashen cewa zan haifi yan Uku, wato lokacin cikin na wata Bakwai tun a wannan lokacin ne naga kamar hankalin mai gidana ya Tashi, yakuma soma kokawa. Yanzu ga shi baya nan, kuma ina cikin wani hali, ga rashin abinci mai gina jiki, ga ba wani abun da zan basu. Gaskiya ina son a taimaka min.” Ta ci gaba da cewa kullum aka bugawa mijinta waya sai yace gashin nan zuwa, amma yanzu kusan mako guda bashi ba Labarinsa.
Friday, 8 February 2019
Home ›
›
TALAUCI wani Magidanci yi batan dabo bayan da aka haifa masa 'yan ukku
Subscribe Our Channel
Subscribe to:
Post Comments (Atom)


No comments:
Write Please Share a Your Opinion.