Maganar Gaskiya : Babu Inda na taba furta cewa "Iya Yawan Kuri'un 'Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri'un 'Yan Darika, Cewar Sheik Kabiru Gombe. .....Ya kuma kalubalanci a kawo muryarsa inda ya fadi haka Daga Ibrahim Baba Suleiman Shahararren Malamin nan Sheikh Kabiru Gombe yace bai taba furta cewa Iya Yawan Kuri'un 'Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe ba, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri'un 'Yan Darika" Shehin Malamin yace wannan karya ce da kirkiran Labarin karya irin na 'Yan shi'a.
"Duk wa'azin da IZALA take gabatarwa
akwai kaset na wa'azin, dan haka mun Kalubalanci wadanda suka kirkiri labarin dasu saka Murya ko Video na inda muka fadi haka, in kuma basu kawo ba zaku gane cewa zunzurutunmakaryata ne "Inji Shi" Kazalika ana kara Jan hankalin mutane da su kara lura tunda zabe ya kusa zuwa, makiya sun dinga kirkirar labaran karya suna yadawa akan Malaman Sunnah, saboda kiyayyar su da Sunnah, da kuma shugaba Buhari, amma ta Allah ba tasu ba. Su wadannan makaryata, idan sunje wajen kiristoci ce musu sukeyi wai Buhari zai musuluntar da Naijeriya. Dan Haka shehin Malamin ya nemi jama'a da suyi watsi da wannan zancen, kuma yace IZALA tana nan akan matsayarta na zaben shugaban kasa ranar asabar a futo a zabi Muhamnadu Buhari
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.