Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun
Obasanjo ya ce, ya sauya matsayinsa na
rashin goyon bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019. Mr. Obasanjo ya bayyana haka ne bayan ziyarar da Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka kai masa a gidansa da ke birnin
Abeokuta.
Obasanjo ya ce, ya yi amanna cewa, Atiku ya daidaita kansa kuma a yanzu haka ya cancanci samun goyon bayansa a zaben kasar mai zuwa. Tsohon shugaban na Najeriya ya taya murna ga
Atiku game da nasarar da ya samu ta wakiltar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, in da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari na
jam’iyyar APC. A can baya dai, Obasanjo ya lashi takobin rashin mara wa Atiku baya wajen fafutukarsa
ta ganin mafarkinsa na zama shugabban kasa ya zama gaske.


No comments:
Write Please Share a Your Opinion.