. Dalilai 5 da kesa haihuwar tagwaye Mutane da yawa dai suna matukar sha'awar yan biyu. - hausanet hausanet





Sunday, 14 October 2018

Home › › Dalilai 5 da kesa haihuwar tagwaye Mutane da yawa dai suna matukar sha'awar yan biyu.

Subscribe Our Channel




(1) Idan ka/kin gada
Ko shakka babu ana gadar haihuwar
tagwaye kamar yadda wannan wani
sanannen abu ne a rayuwar mu ta yau
da kullum. Mutanen da suka fito daga
gidan da ake da yan biyu a lokuta da
dama sukan haifi yan biyu su ma


(2) Shan magunguna
Yanzu haka dai ci gaban kimiyya ya
karu inda akwai wasu magunguna da
ake bayarwa a asibiti da suke
taimakawa ma'aurata wajen haihuwar
tagwaye. Kawai ma'aurata masu
sha'awa sai su garzaya wajen likitan su
yayi musu bayani


(3) Yanayin abinci
Sanin kowa ne cewar abinci yana da
matukar muhimmacin a wurin tafiyar
da rayuwar dan adam. Bincike yanuna
cewar mata dake cin abinci mai
madara-madara koma madarar kanta
suna da yiwuwar samun tagwaye fiye
da wadanda basu ci.
Akwai wata nau'in doya ma da ke
akwai a kasar yarbawa wadda akayi
imanin cewa tana sa haihuwar
tagwayen


(4) Kabila
Ita kabila tana da matukar anfani a
wajen haihuwar tagwaye. Wata kabilar
an santa sosai wajen haihuwar an biyu
fiye da wata


(5) Shekaru da kuma girman jiki
Bincike ya nuna cewar manyan mata
sun fi haihuwar yan biyu fiye da yara
kuma marasa kiba. An dai gano cewar
matan da suka haura shekaru 30 sun fi
haihuwar tagwaye to muma Allah ya bamu