Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin korar kocinsa Julep Lepotegui nan da karshen wannan wata
Jaridar AS ta Sifen ta ruwaito cewa tuni
mahukunta kulob din suka fara tunanin kocin da zai maye gurbinsa da zarar sun kore shi
. Jaridar ta kara da cewa daga cikin kocin da kulob din ya fara zawarci sun hada da tsohon kocin Chelsea
Antonio Conte. A ranar 28 ga wannan wata da muke ciki ne
kulob din zai yi wasa mafi zafi da FC Barcelona, wasan da ake wa lakabi da “El-Clasico”. Masana harkar kwallo sun yi hasashe daga ranar ce kocin zai san matsayinsa, na ci gaba da zama
ko kuma a sallame shi
Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna mahukunta kulob din sun fara yunkurin cefano zaratan ’yan kwallo da zarar an bude kakar cinikin ’yan kwallo a watan
Janairu.
Daga cikin ’yan kwallon da kulob din zai fi mayar da hankali wajen sayo su akwai Neymar da ke buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) da kuma dan kwallon Tottenham da ke Ingila
Christian Eriksen.
Kulob din ya ce zai yi haka ne don ya karfafa.gwiwar ’yan wasansa da yanzu haka suke fuskantar matsala tun bayan da Cristiano Ronaldo ya bar kulob din Madrid ya koma na Jubentus
da ke Italiya a kakar wasa ta bana. Neymar wanda ya canza sheka daga kulob din FC Barcelona na Sifen zuwa na PSG da ke Faransa kimanin shekaru biyu da suka gabata, rahotanni sun nuna
akwai yiwuwar ya canza sheka zuwa kulob din Madrid idan ya samu damar yin haka.
Kar kaman ta kana shafin www.hausanet.ml
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.